Kotun Koli ta sanya gobe Alhamis a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da Peter Obi suke kalubalantar nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.
Atiku wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya shigar da karar ne kamar takwarana na Jam’iyyar LP, Mista Peter Obi.
Atiku da Peter Obi kowannensu na ikirarin shi ne ya lashe zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 da kuri’u mafiya rinjaye, duk da cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Tinubu ne ya yi nasara, aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Daraktan Yada Labarai na Kotun Koli, Festus Akande ya sanar a ranar Laraba cewa a ranar Alhamis alkalan kotun za hu yanke hukunci kan shari’ar zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.
A ranar Litinin PDP da LP da ’yan takararsu suka gabatar da shaida a gaban kotun koli, wadda ta yi watsi da karar Jam’iyyar APM da dan takararta, Chichi Ojei, bayan sun janye kararsu.