✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare ta a kurkuku kan kisan jiririn kishiyarta

Kotu ta tsare wata matar aure a gidan yari kan zargin kashe jaririn kishiyarta ta hanyar shayar da shi maganin kwari a Jihar Kano.

Kotu ta tisa keyar wata matar aure zuwa gidan yari kan zargin ta da kashe jaririn kishiyarta a Jihar Kano.

Mai sharia Zuwaira Yusuf Ali na Babbar Kotun Jihar Kano Mai lamba 16 ne ya ba da umarnin bayan gurfanar da matar auren daga Karamar Hukumar Kunci bisa zargin kisan jaririn.

Mai gabatar da kara, lauyan gwamnatin jihar, Barista Abba Lamido Sorondinki ya shaida wa kotun cewa matar ta kashe jaririn dan kimanin kwana 18 ne ta hanyar shayar da shi da maganin kwari, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Bayan sauraron jawabin, alkalin kotun, Mai sharia Zuwaira Yusuf Ali ta bayar da umarnin tsare wacce ake zargin a gidan yari har zuwa ranar 2 ga watan Disamba 2023 don ci gaba da sauraren shari’ar.