Kungiyar Malam Jami’a (ASUU) na tunanin maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan yanke albashin watan Oktoba da aka yi wa lakcarori.
Bayan taron gaggawa da kungiyar ta kammala a safiyar Talata, Shugaban ASUU na Kasa, Farfesa Emmanuel Osedeke, ya soki biyan su albashin kwana 18, yana mai cewa su ba ma’aikatan wucin gadi ba ne ballantana a ce iya ranakun da suka yi aiki kadai za a biya su.
- Cire ilimin jima’i daga manhajin karatu ba daidai ba ne —Kungiyoyi
- 2023: Kotu ta hana PDP shiga takarar gwamnan Zamfara
- Ban karbi addinin musulunci ba —Drogba
Farfesa Osedeke ya ce, “Kungiyar za ta ci gaba da bin matakan da doka suka dace na shawo kam matsalar ba tare da ta sarayar da muradu da kuma walwalar malaman jami’a ba.”
Duk da cewa bai ce uffan game da shiga sabon yajin aiki ba, Farfesa Osedeke, ya yi kira ga iyaye da dalibai da sauran ’yan Najeriya da su fahimci matsayin lakcarorin.
A cewarsa, biyan su iya kwanakin da suka yi aiki kamar ma’aikatan wucin gadi, abu ne da ba a taba yi ba a taririn aikin koyarwa a jami’a.
Amma abin da gwamnati ta yi musu na biyan albashi kamar masu aikin wucin gadi na bukatar su dauki matakin doka.