✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ASUU na taron gaggawa kan rikicin albashi

Shugabna ASUU na Kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ke jagorantar zaman, kuma ana sa ran zai yi wa manema labarai bayani daga baya.

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta fara taron sirri kan matakin da za ta dauka kan yanke albashin da aka biya lakcarori a watan Oktoba.

Majalisar Zartarwa (NEC) ta ASUU ta shiga taron gagagwan ne a sakatariyar kungiyar da ke Jami’ar Abuja a ranar Litinin.

Shugabna ASUU na Kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ke jagorantar zaman, kuma ana sa ran zai yi wa manema labarai bayani daga baya.

Wani mamban Majalisar da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana mana gabanin zaman cewa za a sanar da ’yan jarida game da sauran batutuwa idan suka kammala taron na ranar Litinin.

%d bloggers like this: