✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘ASUU ba za ta bar shiga yajin aiki ba sai gwamnati ta yi abin da ya makata’

Ƙungiyar ASUU ta yi bore kan shirin Asusun Kula da manyan makarantu (TETFUND) na sanya jami'o'i masu zaman kansu a cikin masu cin gajiyar tallafinta

Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta ce “za ta ci gaba da shiga yajin aiki, har sai lokacin da gwamnati ta yi abin daya dace,” a bangaren manyan makarantu.

Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana haka ne a yayin da yake bore kan shirin Asusun Kula da Jami’o’i (TETFUND) na shigar da jami’o’i masu zaman kansu cikin masu cin gajiyar tallafinta.

Farfesa Osodeke ya shaida wa taron masu cin gajiyar tallafin TETFUND cewa shigo da jami’o’i masu zaman kansu a cikin tsarin zai haifar da yawaitar su ba tare inganci ba.

Ya bukaci TETFUND ta rika tsananta bincike tare da hukunta duk masu gajiyar tallafinta, saboda wasunsu ba su amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata ba.

Da yake nasa jawabin, Shugaban TETFUND, Sunday Echono, ya ce an kira taron ne domin tattauna hanyoyin inganta harkar ilimi a bangaren gaba da sakandare.