Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’o’i da sauran manyan makarantun Gwamnatin Tarayya su dakatar karin kudin rajistarsu.
’Yan Najeriya dai na ta korafi bisa yadda jami’o’i da sauran makarantun gwamnatin suka kara kudaden rajistarsu fiye da kima, inda a wasu wuraren aka ninka kudaden fiye da sau 10.
- NAJERIYA A YAU: Shin Da Gaske Gwamnatin Kano Na Shirin Dawo Da Sarki Sanusi II?
- An cafke Alkalin da ya yi shigar mata yana zana wa budurwarsa jarrabawa
Tinubu ya ce daina kara kudin rajista da makarantun suke yi yadda suka ga dama ya zama dole, domin saukaka wa iyaye da kuma tabbatar da ganin kowane dalibi ya samu ilimi mai zurfi, kamar yadda ya yi alkawari.
Ya kuma ba da umarnin raba bas-bas ga kungiyoyin dalibai a daukacin jami’o’i kwalejojin ilimi da na fasaha, domin rage wa iyaye da dalibai tsadar kudin sufuri.
Kakakin shugaban kasa, Dele Alake, ta wata sanarwa ranar Litinin ya ce shugaban ya sa hannu kan umarnin cire duk sharaddan da za su kawo tarnaki wajen ba wa dalibai rancen za a fara daga sabuwar shekarar karatu mai kamawa a watan Satumba.
Sai dai har yanzu gwamnatin ba ta fayyace tanadi ko tsarin da ta yi a kasa na fara bayar da rancen ba, ko yadda za ta aiwatar da shi da kuma tabbatar da cewa daliban wadanda da suka cancanta ne suka samu kuma babu cuwa-cuwa.
Ana iya tunawa a makon jiya fadar shugaban kasar ta kekashe kasa cewa kudin rajista da jami’o’i suke karba daga dalibai ya danganta da makarantar; sai dai kuma jama’ar kasa na kokawa kan yadda abnin ya wuce misali.
Dokar ba wa dalibai rancen da Tinubu ya sanya hannu a kai ta tanada ba wa dalibai rancen daukar nauyin karatunsu, muddin kudaden shigarsu ba su haura Naira dubu 500 ba.
Sai dai ta haramta bayar da rancen ga duk dalibai da aka samu a baya ya ki biyan ba shi, ko kuma iyayensa sun ki biyan bashin da suka karba.
Haka kuma, dalibai masu rauni za su ci gajiyar tallafin kudi da kuma abincin da shugaban kasar ya sa a raba metric ton 200,000 daga rumbunan ajiyar hatsin gwamnati da ke fadin Najeriya.