Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta ce akalla jami’o’in kasashen waje 270 ne yanzu haka suke neman a ba su lasisin kafa jami’o’i a Najeriya.
Shugaban hukumar na kasa, Dokta Chris Maiyaki, ne ya bayyana haka yayin wani taron kara wa juna sani da Hukumar Raya Al’adun Birtaniya ta shirya a Abuja ranar Alhamis.
- Majalisa ta bukaci gwamnati ta kafa hukumar kayyade farashin kayayyaki
- NAHCON ta ba maniyyata Aikin Hajjin badi mako 3 su fara biyan kudadensu
Ya kuma ce tuni Gwamnatin Tarayya ta bude kofarta domin ta ba jami’o’in kasashen waje dama su shigo a dama da su a fannin ci gaban ilimi a Najeriya a kokarinta na inganta fannin.
Dokta Chris ya ce sun dauki matakin ne domin ganin karatun jami’o’in Najeriya ya yi kafada da kafada da na kowacce kasa a duniya, inda ya ce dama haka ya kamata tsarin karatun jami’o’i ya zama.
Shugaban na NUC ya ce, “Duk da jami’o’i sama da 270 din da muke da su a Najeriya, har yanzu muna aikin ganin mun fadada adadin, yanzu haka ma akwai jami’o’in waje sama da 270 da ke neman a basu lasisin kafawa a Najeriya.”
Kodayake ya ce akwai tsauraran sharudan da dole sai an cika su kafin su ba da lasisin, amma ba zai yiwu su ci gaba da rufe kofofinsu ga makarantun ba.
Tun da farko, Daraktan Shirye-shirye na hukumar ta Birtaniya a Najeriya, Chikodi Onyemerela, ya ce an shirya taron ne da nufin ganin an samu alaka da hadin gwiwa tsakanin jami’o’in Najeriya da na Birtaniya domin su yi aiki kafada da kafada.