✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya yi sabbin naɗe-naɗe

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya (NUC). Haka na ƙunshe cikin wata…

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya (NUC).

Haka na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar a yammacin wannan Juma’ar.

Farfesa Ribadu — wanda ƙwararren masanin lafiyar dabbobi ne — ya taɓa riƙe Shugaban Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Yola da kuma Jami’ar Sule Lamido da ke Jihar Jigawa.

Haka kuma, sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya naɗa Shugaban Jami’ar Al-Istiqamah da ke Kano, Farfesa Salisu Shehu a matsayin Shugaban Majalisar Binciken Ilimi da Ci gaba ta Najeriya (NERDC).

Farfesa Shehu ƙwararren malamin halayyar ɗan Adam.

Shuagba Tinubu ya kuma naɗa Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri a matsayin Shugaban Hukumar Tallafawa Ci gaban Ƙasashen Afirka (NEPAD).

Jabilu Tsauri ya yi digirinsa na biyu a fannin harkokin kasa da kasa da diflomasiyya a Jami’ar Ahmadu Bello.

Gogaggen jami’in gudanarwa ne wanda ya ƙware a harkokin majalisa, siyasar duniya, da mulkin dimokuraɗiyya.

Kazalika, Shugaba Tinubu ya naɗa Yazid Shehu Umar Ɗanfulani a matsayin Babban Sakataren Hukumar Haƙar Ma’adanan Zinare (SMDF/PAGMI).

Shi ma dai Yazid Ɗafulani ya yi digirinsa na farko a fannin gudanar da kasuwanci da kuma digiri na biyu a fannin fasaha da gudanarwa a Jami’ar Hertfordshire da ke Birtaniya.