✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rage shekarun shiga jami’a zuwa 16 a Najeriya

JAMB ta sanya 140 a matsayin mafi karancin maki don shiga jami’o’i a shekarar 2024

Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya ta amince da shekaru 16 a matsayin mafi karanci ga dalibai da ke neman shiga Jami’a.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya sanar cewa za a fara daukar dalibai masu shekaru 16 a makarantun gaba da sakandare ne daga shekarar 2025.

Ministan ya sanar da haka ne a Abuja a wurin taron Masu Ruwa da Tsaki kan harkar shiga manyan makarantun, wanda Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i ta Kasa (JAMB) ta shirya.

Ya sanar da rage shekarun zuwa 16 ne bayan mahalarta taron sun tayar da hayaniya a lokacin da aka bayyana musu cewa shekaru 18 shi ne mafi karanci da doka ta kayyade domin shiga manyan makarantu.

An yayin taron Hukumar JAMB ta sanar da 140 a matsayin mafi karancin maki don shiga jami’o’i a shekarar 2024.

Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Is-haq Oloyede, ya kara da cewa maki 100 ne mafi karanci ga masu son shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha da Kwalejojin Ilimi.

Sai dai, Farfesa Oloyede ya bayyana cewa makin da aka ambata sune mafi ƙanƙanta, amma hakan ba yana nufin dole ne manyan makarantu ba za su iya karawa ba.

Ya ci gaba da cewa sun amince da cewa makarantu su rika karbar kudi N2,000 don tantancewar dalibai domin jarabawar Post UTME a yanzu.

Oloyede ya bayyana cewa hukumar za ta ba su bayanan dalibai domin rage musu kushe kudi.

Hukumar ta JAMB ta kuma ce a soke wa masu neman shiga manyan makarantun kasar waje da fursunoni da nakasassu zana Post UTME.