✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAHCON ta ba maniyyata Aikin Hajjin badi mako 3 su fara biyan kudadensu

Ta ce duk wanda bai biya kudin ba kafin lokacin, shi ya jiyo

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ce kasar Saudiyya ta ba maniyyatan kasar nan mako 3 su fara biyan kafin alkalami na kudaden kujerar Aikin Hajjin shekara ta 2024.

A cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Alhamis, ta ce Saudiyya ta ajiye ranar 4 ga watan Nuwamba domin kammala shirye-shiryen da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar.

Ta ce bayan nan ne hukumar za ta tantance ainihin yawan maniyyatan wanda daga nan ne za ta tattauna batun farashin kujera, har kuma ta yanke shi daga karshe.

Fatima ta kuma ce shirye-shiryen da hukumar ta fara yi ne suka sa a yayin tattaunawar shugabannin Hukumomin Alhazai na jihohin Najeriya a kwanakin baya ta sanar da Naira miliyan 4 da rabi a matsayin kudin kujera a hajjin badi.

Sanarwar ta ce, “Da farko dai dalilai uku ne suka sa za a fara ajiye wadannan kudaden na kafin alkalami. Na farko shi ne saboda jihohi su san yawan alhazan da za su biya kudin, akalla kafin nan da ranar 4 ga watan Nuwamba, wanda shi ne lokacin da Saudiya ta sanya domin kammala shirye-shiryen dukkan masu ruwa da tsaki.

“Yin hakan zai taimaka wa hukumomin yin dukkan tsare-tsaren da suka kamata a kan lokaci.”

Sai dai ta ce an amince daga busani za a ba maniyyatan dama su cika ragowar kudaden sannu a hankali zuwa lokacin da za a sanar da ainihin farashin kujerar.

Ta kuma ce duk wadanda suka gaza biyan adadin da aka fara kayyadewa, to su kuka da kansu idan aka kirga yawan maniyyatan babu sunansu.

Sai dai ta tsaya kai da fata cewa har zuwa wannan lokacin, akwai yiwuwar mafi karancin farashin kujerar a badi ya kai Naira miliyan hudu da rabi, kamar yadda hukumar ta sanar a kwanakin baya.