Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) da takwararta ta Ma’aikatan Jami’ar da ba Malamai Ba (NASU) sun ayyana shiga yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai tun daga ranar 18 ga wannan wata na Maris.
Kungiyoyin sun ce za su tsunduma yajin aikin ne domin yi wa Gwamnatin Tarayya matsin lamba kan biyan albashin watanni hudu da ta rikewa mambobinsu sakamakon yajin aikin gamagarin da suka shiga a shekarar 2022.
- Ban mayar da hankali kan ɗora wa gwamnatin da ta shuɗe laifi ba —Tinubu
- Sojin Nijar za su saki Bazoum
Kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin biyu, ya ce shiga yajin aikin na daga cikin shawarwarin da ya cimma, bayan wani taro da ya gudanar a birnin Akuren Jihar Ondo a karshen makon da ya gabata.
Shugaban kungiyar SSANU, Muhammad Ibrahim, wanda ya karantawa manema labarai sanarwar bayan taro a Abuja a ranar Litinin, ya ce an yanke shawarar shiga yajin aikin ne a matsayin matakin karshe kasancewar takardun korafe-korafe da sauran sakonni tsakaninsu da gwamnatin tarayya ba su samar da kyakkyawan sakamako akan bukatar biyan albashin da aka rike musu ba.
A cewar sanarwar, “matukar gwamnatin tarayya ta kasa daukar matakin warware wannan matsala tare da yin martani ga sakonnin da muka aike mata, ya zama wajibi mambobin kungiyoyin biyu su gudanar da ganawar gaggawa domin daukar tsauraran matakan da doka ta aninta dasu domin warware matsalar.
Al’amarin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin ke zargin Gwamnatin Tarayya da yi wa batun mambobinsu rikon sakainar kashi.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a watan Oktoba na bara ne Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ba da umarnin biyan ma’aikatan jami’o’i albashin da aka rike musu sakamakon yajin aikin da suka yi a shekarar 2022.
Sai dai gamayyar kungiyoyin ASUU da NASU har ma da takwararsu ta ma’aikatan da ke fannin kirkire-kirkire suka yi ikirarin cewar har yanzu basu ga albashin da aka rike musun ba tare da ba da wa’adin mako guda makonni biyu da suka gabata.
SSANU da NASU sun ce sun yi dukkanin mai yiyuwa domin hana mambobinsu shiga yajin aikin da nufin ci gaba da samun wanzuwar zaman lafiya da daidaituwar al’amura.
A bayan nan ne yayin wata hirarsa da Gidan Talbijin na Channels, Shugaban SSANU ya bayyana cewa, “Mu ne masu kula da harkokin tsaron jami’o’in da gudanar da mulki da kula da likitoci da dakunan kwanan dalibai da wutar lantarki da tafiyar da komai bayan koyarwa.
“Don haka da zarar mambobinmu sun daina aiki, babu wata jami’a da za ta iya aiki a Najeriya.