Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) Mohammed Ibrahim ya ce za su tafi yajin aiki idan gwamnati ta ki biya musu bukatunsu nan da kwanaki bakwai.
Ya bayyana cewa za su shiga yajin aikin ne tare da wasu kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i biyu na kasar nan
Ibrahim ya ce, sun ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki bakwai, daga ranar Litinin 4 ga Mayu, 2024
Da ake hira da shi a gidan talabijin na Channels TV ranar Lahadi, ya yi barazanar cewa kungiyoyin za su rufe jami’o’in gaba daya, idan gwamnatin ba ta yi wani abu ba a karshen wa’adin.
- Mutum 12 sun rasu, 28 sun ji rauni a hatsarin mota a hanyar Kano
- 95% Na Ainihin ’Yan Boko Haram Sun Mutu –Gwamnatin Borno
“Mu ne masu kula da harkokin tsaron jami’o’in da gudanar da mulki da kula da likitoci da dakunan kwanan dalibai da da wutar lantarki da tafiyar da komai bayan koyarwa, don haka da zarar mambobinmu sun daina aiki, babu wata jami’a da za ta iya aiki a Najeriya.