✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Asalin rubutun boko da bunkasar harshen Hausa (4)

Ita ma kasar Damagaram, wadda a yanzu da kasar Hausa ake kiranta, asalinta an ce wani mafarauci ne mai suna Zundurma ya fara zama a…

Ita ma kasar Damagaram, wadda a yanzu da kasar Hausa ake kiranta, asalinta an ce wani mafarauci ne mai suna Zundurma ya fara zama a wurin. Sannu a hankali Bare-Bari suka rika kwararowa yankin saboda an ce wajen ya kasance turbar kasuwanci ce, har kuma daga bisani aka samu karin kabilu mabambanta, wadanda mafi akasari yanzu duk sun rikide sun koma Hausawa. 

A hakika, a cikin Hausa ta yau akwai Bare-Bari da yawa, yawan nasu ma ba zai lissafu ba; tun da an samu cewa akwai garuruwa da dama wadanda Bare-Bari ne suka kafa su. Yawa-yawan wadancan Bare-Bari, wani dalilai ne ya taso da su zuwa kasashen Hausa, sai ga shi kuma bayan zamani mai tsawo ya shude, jikokinsu duk sun zama Hausawa, jinin jikinsu kadai ne na Kanuri (duk da shi ma ya gauraya da na sauran kabilu) amma harshe da al’ada duk da na Hausa suke amfani. 

Irin wadannan misalan ne a Daura da Zamfara da Gobir da Maradi da mafi yawan jihohin Hausawa. Abin tambaya dai a nan shi ne, yaya aka yi harshen Hausa ya hadiye yarukan wadancan kabilu, ta yadda a yanzu suka zama tarihi?

To, a bisa ga falsafar marubucin tarihi Ibn Khaldun, ana gane abin da ya faru a baya ta hanyar fahimtar abin da ke faruwa a yanzu, sannan za a iya gane mene ne zai faru a nan gaba idan aka yi duba na tsanaki bisa abubuwan da ke faruwa a yanzu. A saboda haka, na fi ganin abubuwa biyu ne manya wajen zamowa silar bunkasar harshen Hausa.

Na farkon shi ne rashin kyamar bakon abu matukar bai zo da abu sabanin fahimtarsu ba. Na biyu kuwa shi ne karbar bako tare da mai da shi dan gida.

Ga abinda aka rubuta a littafin ‘Waka A Bakin Mai Ita’ dangane da wannan: “Wani abin sha’awa shi ne, harshen Hausa harshe ne mai iya karbar kowanne irin salo da harshen Larabci ya zo da shi ya zauna darandam kamar an an aka halicce shi…”

Da yake littafin yana magana ne a kan kamanceceniyar ma’aunan gwajin wakar Larabci da ta Hausa amma muna iya cewa wannan abin ba a kan Larabci da waka kadai ya tsaya ba, domin idan za a yi bincike za a samu cewa harshen Hausa ya yi aro na kalmomi da hikima daga harsuna mabambanta kuma sannu a hankali ya mayar da abin da ya aro din ya zauna daram kamar dama tun can asali akwai shi. 

A wani gagarumin bincike da aka yi, Dokta Aliyu Abubakar ya rubuta a littafinsa ‘Al-thakafatul Arabiyya fi Nigeria’ cewa yawan kalmomin Larabci a cikin Hausa sun kai khumusi (1/5. To idan kuwa da za a auna da sauran yaruka da watakila a ga wai ina ainihin Hausar take? Ko kuma idan za mu yi hasashe, za mu iya duba cewar Larabawa sun fara shigowa kasashen Hausawa don mu’amala tun a waje karni na 13 ne. Don haka muna iya cewa a iya shekaru 700 na mu’amala tsakanin Hausawa da Larabawa (1300-2000), tarin kalmomin da Hausa ta ara  sun kai khumusi. Ke nan, idan muka dauki wancan ma’aunin auna lamurori da Ibn Khaldun ya ba mu, za mu iya cewa daga karni na 7 zuwa 13, Hausa ta ari wasu kalmomin da adadinsu zai iya riskar khumusi ko wani abu da ke sama ko kasa da haka daga wasu harsunan, wadanda zuwa yanzu zai yi wuya mu gane su.

A baya-bayan nan kuma, shigowar Turawa da fara mu’amalarsu a kasar Hausa ta soma ne daga shekarar 1900. Zuwa yanzu muna iya cewa harshen Ingilishi ya shiga cikin Hausa a iya wadannan shekaru 200 da adadin kalmomi masu tarin yawa, ta yadda za ka samu matasanmu zai yi wuya su yi sa’a guda suna hira ba tare da sun yi amfani da kalmar aro ta Ingilishi ba. Watakila kamar haka Hausa ta soma a sauran yarukan kuma muna iya cewa nan da shekaru 500 masu zuwa tsoffin kalmomin Hausa da yawa na iya dulmiyewa, tun da an samu musayarsu da na Ingilishi.

Don haka, muna iya ganin cewa daukacin kabilun da ke tare da Hausawa tun tale-tale sun rika aron kalmomin Hausa ne, yayin da su ma kuma Hausawa na dauri suka rika aron kalmomi daga gare su. A haka har lokaci ya yi da Hausa ta hadiye yawa-yawan yarukan, ta kuma mayar da yawa-yawan kalmomin aro mallakinta.

Watakila kuma saukin Hausa wajen yarawa da arowar kalmomi ya sa makwabtansu suka fara koyon Hausa a sannu-sannu lokaci mai tsawo da ya shude har takai jallin da harshen Hausa ya zame musu dan tsakiya wajen saduwa tsakanin kabilun da ke da bambancin yare da juna.  

Zuwa yanzu dai akwai kabilun da sun ma mance da ainihin harshensu, da Hausa kurum suke amfani, yayin da wasu kuma suka rike nasu harshen suka kuma riki harshen Hausa; ta yadda idan ba su yi hankali ba, shekaru da dama masu zuwa harshen Hausa zai hadiye nasu kamar yadda ya yi wa wadancan yaruka na baya. 

Wannan a takaice na iya zama wani abin kamawa dangane da bunkasar harshen Hausa a wannan yanki namu.

Gwarzo ya rubuto daga Kano (08060869978)