Kamar yadda doka ta tanada cewar duk wata ƙaramar hukumar a tabbatar da cewa zaɓaɓɓun shugabanni ne ke jagorancin ta Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Katsina KTSEIC ta sanar da gobe Asabar ne za a gudanar zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Wannan ya sa Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Raɗɗa ta shirya aiwatar da zaɓen ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin jahar wanda hakan zai ƙara ba su damar cin gashin kan su kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar.
- Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano
- Shugaban Ƙungiyar Afenifere, Adebanjo ya rasu
Kamar yadda shugaban Hukumar zaɓen mai zaman kanta ta Jihar Alhaji Lawal Alhassan Faskari ya shaidawa manema labarai a lokacin da ake rarraba kayan zaɓen zuwa ƙananan hukumomin jihar ya ce, tuni hukumar zaɓen ta kammala duk wasu shirye-shirye don ganin anyi zaɓen bisa doka.
Hakan ya sa aka ba kowace jam’iya damar fito da wanda zai yi mata takarar kujerar ƙaramar hukumar ko ta Kansila. Sai dai abin da mafi yawan jama’a suka yi tsammani cewar babbar jam’iyar adawa ta PDP ba za ta shiga zaɓen ba bisa dalilanta na cewa, ba sahihin zaɓe ne za a yi ba.
Duk da hakan bai hana wasu jam’iyun shiga cikin wannan zaɓe ba. Jam’iyar Accord da Booth da AAC da ADC sun shiga cikin wannan zaɓe.
Dangane da wuraren da ake fama da matsalar tsaro kuwa, an shirya gudanar da yin zaɓukan su a wasu wurare da aka tanada a yankunansu kamar yadda aka yi a zaɓukan da suka gabata.
Duk da haka kuma hukumomin tsaro a jihar sun ja hankali tare da gargaɗi ga masu ƙoƙarin kawo wata fitina da gargaɗin su ko su fuskanci fushin hukuma.
Kazalika, an hana zirga zirgar ababen hawa in baya ga na musamman da kuma masu gudanar da aiyukan zaɓen.