Arsenal ta yi wa Manchester United dukan koshi da ci 3-1 a wasan mako na huɗu a Premier League da suka kara a Emirates ranar Lahadi.
A minti na 27 da take leda Marcus Rashford ya fara ci wa United kwallo ya zama na biyu a United da ya ci Arsenal a wasa uku a jere, bayan bajintar Robin van Persie tsakanin 2012 zuwa 2013.
Minti ɗaya tsakani Martin Odegaard ya farke kuma daf da za a tashi Declan Rice ya ƙara na biyu, sannan Gabriel Jesus ya ci na uku.
Da wannan sakamakon Arsenal mai maki 10 ta ci wasa uku da canjaras daya, shi ne wanda ta yi 2-2 da Fulham a makon jiya
Man United mai maki shida ta ci wasa biyu an doke ta fafatawa biyu da fara kakar bana.
A ranar 17 ga watan Satumba Arsenal za ta ziyarci Everton, yayin da United za ta karbi bakuncin Brighton ranar 16 ga watan na Satumba.