✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba Gida-Gida zai aurar da Murja Kunya

Matar da ta fito ta ce tana son a inganta sunna ta Manzon Allah ai ba a bar kyama ce.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya sanar cewa ya shirya tsaf domin aurar da fitacciyar jarumar nan ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.

Abba Gida-Gida wanda ya sanar da hakan a Fadar Gwamnatin Kano ya ce zai aurar da jarumar ce a cikin zawarawan da gwamnatinsa ke shirin aurarwa kwanan nan.

Gwamnan ya ce zai yi wa Murja wannan tagomashi ne la’akari da gudunmawar da ta rika bai wa gwamnatinsa tun gabanin ya lashe zaben da aka yi a watan Maris, har zuwa yanzu.

A cewarsa, “kowa ya san irin rawar da Murja ta taka wajen yayata ayyukan alheri da gwamnatin nan ke yi, wanda babu abin da za mu ce sai son barka.

“Kuma ita ce ta fara fitowa a cikin ’yan group dinsu [’yan TikTok] ta ce tana son a yi mata aure sunnar Manzon Allah.

“Matar da ta fito ta ce tana son a inganta sunna ta Manzon Allah ai ba a bar kyama ce.

“Kuma so take ta je inda za ta ba da gudunmawar inganta addinin Musulunci.

“Auren zawarawa dai mun shirya tsaf, kuma muna jiran Murja ta kawo mana angon, mu kuma in Allah Ya yarda za mu yi abin da ya kamata,” a cewar Gwamnan.