✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Arjen Robben ya zura kwallonsa ta 100 a kulob din Bayern Munich

Shahararren dan kwallon Holand da yanzu haka yake buga wa kulob din Bayern Munich na Jamus kwallo, Arjen Robben a ranar Talatar da ta wuce…

Shahararren dan kwallon Holand da yanzu haka yake buga wa kulob din Bayern Munich na Jamus kwallo, Arjen Robben a ranar Talatar da ta wuce ne ya samu nasarar zura kwallonsa ta 100 a gasar rukunin Bundesliga na Jamus. A wasan da kuloh din ya yi da na Freiburg, Munich ce ta samu nasara da ci 2-0. Robben ne ya zura kwallon farko yayin da Thomas Muller ya zura ta biyu.

Haka kuma a ranar Asabar da ta wuce ne Robben ya zura kwallaye biyu daga cikin kwallaye hudu da kulob din ya zura a ragar Augsburg.
Kocin Bayern Munich, Pep Guardiola tuni ya bayyana Robben a matsayin dan kwallon da babu wanda ya kama kafarsa a kulob din a kakar wasa ta bana.
Kawo yanzu kulob din Munich bai samu rashin nasara a wasannin da ya yi a gasar Bundesliga ta Jamus ba.