Gidauniyar Arida ta bai wa marayu da talakawa kimanin dubu uku tallafin kayan abinci domin rage masu radadin yunwa a jihar Kaduna.
Shugabar Gidauniyar Arida, Hajiya Rabi Salisu Arida, ce ta jagoranci raba kayan tallafin abincin ga marasa galihu, wadanda suka hada da: Shinkafa da gero da sigari da Taliya da makaroni da man gyada.
Daruruwan marayu da mabukata ne da ke zaune a garuruwan Maraban Jos da Jaji da sauran kauyuka suka amfana da wannan tallafin.
Ta kuma bayyana cewa, mutum ko ba maraya bane indai bashi da karfi kuma yana da tsananin bukatar abinci an bashi domin rage masu radadin dokar hana fita sakamakon hana yaduwar cutar coronavirus da kuma azumin Ramadan.
- Jinjina ga uwar marayun Kaduna
- An bukaci masu hali da su tallafawa talakawa
- Yadda baban Marayu ya zama Sufeto Janar na ’Yan sanda
“Mun fara ne daga garin Maraban Jos inda aka rabawa mabukata kusan dari biyar sannan a unguwar NDC aka bai wa mutum kusan dari biyu da wani abu sannan muka shiga unguwar Hayin Banki da Kawo aka rabawa daruruwa, sai muka shiga garin Jaji inda mata da maza da nakasassu suka amfana.
” Kuma Insha Allahu zamu ci gaba da wannan aiki na taimako ga mabukata nan da bada dadewa ba. Idan Allah Ya yarda muna da bukatar hade dukkan kananan hukumomin jihar, inda muke da marayu da suka yi ragista da mu,” inji ta.