Jam’iyyar APC mai mulki za ta bayyana ranar da za ta gudanar da babban taronta don zaben shugabanninta nan da ’yan kwanaki namsu zuwa kamar yadda wata majiya ta shaida wa Aminiya. Wannan yana faruwa ne bayan da a ranar Talatar da ta gabata Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kara wa shugabannin jam’iyyar wa’adin shekara daya a karkashin shugabancin Oyegun haramtacce ne da ya saba wa doka. Kuma majiyar ta ce a karshen taron Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar an amince da matsayin na Shugaban kasa. A watan Yunin bana ne wa’adin shugabancin shugabannin zai kare, hakan nan nuna jam’iyyar na da kasa da kwana 90 don gudanar da zaben shugabannin mazabu da kananan hukumomi da jihohi da na kasa don zabo sababbin shugabanninta.
A wajen taron, Shugaban kasa ya kada hantar shugabannin da wannan mataki nasa.
A watan jiya ne wani taron shugabannin Jam’iyyar APC ya yanke shawarar cewa shugabanin ba za su sauka ba, sai an gudanar da zaben 2019. Sai dai tun a wancan lokaci, matakin bai yi wa jagoran jam’iyyar ta APC, Bola Tinubu dadi ba, wanda masu kula da al’amuran siyasa ke ganin babu jituwa a tsakaninsa da Shugaban Jam’iyyar, Cif John Oyegun.
Shugaba Buhari ya bayyana wa kusoshin jam’iyyar cewa a soke karin wa’adin da aka yi wa shugabanni a watan jiya, “Domin ya kauce wa dokar jam’iyya da kuma dokar Najeriya.”
Wannan matsaya da Shugaban kasar ya dauka ta zo wa mafi yawan mahalarta taron da mamaki, inda a can baya mafi yawan ’ya’yan jam’iyyar suka amince da karin wa’adin shekara guda ga Oyegun da shugabannin jihohi.
Kuma duk da cewa Jagoran Jam’iyyar APC ta kasa, Cif Bola Tinubu bai halarci taron ba, ya nuna farin cikinsa bisa wannan mataki da Shugaban kasa ya dauka na soke karin wa’adi ga shugabannin jam’iyyar, inda ya bayyana hakan da nasarar dimokuradiyya, sannan ya kara da cewa Shugaba Buhari ya tsamo jam’iyyar daga fadawa cikin rudani.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ba su hakarci taron Kwamitin Zartarwar ba, inda hakan ke haifar da jita-jita kan yiwuwar ana samun taku-saka a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar.