✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

APC za ta samu matsala idan Buhari ya sauka daga mulki —Lawan

Lawan ya bukaci APC ta nemo mafita kafin saukar Buhari a 2023.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, ya yi gargadi da babbar murya cewar jam’iyyar APC na iya fuskantar babban kalubale da zarar Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa a 2023.

Sanata Lawan, ya yi wannan jan kunne ne a yayin taron matasan jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar Litinin, a Abuja.

  1. IPMAN ta dakatar da kai mai zuwa Abuja da wasu jihohi
  2. Rashawa: Kotu ta yanke wa Farouk Lawan daurin shekara 7

“Magana ta gaskiya duk wani goyon baya da muke gani APC na samu, ya samu ne a dalilin Shugaba Muhammadu Buhari, don haka dole mu nemo mafita.

“Dole ne jam’iyya ta nemo mafita kafin karewar wa’adin mulkin Shugaba Buhari a 2023,” inji Lawan.

Shugaban Majalisar Dattawan ya ce Buhari na da rawar da zai taka ko da ya sauka, amma kuma jam’iyyar sai ta fi fuskantar kalubale idan ya gama mulkinsa.

Taron matasan da APC ta gudanar shi ne irinsa na farko da ta yi tun bayan darewar jam’iyyar a mulki a 2015.