Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Femi Fani Kayode wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a ranar Alhamis, ya ce jam’iyyar ta bambanta da ta da.
Tsohon ministan ya ce yana nan a kan bakarsa na ci gaba da sukar APC ta da, wadda yake nadamar shigar ta a 2019.
Bayan sauya shekarsa zuwa APC, tsohon ministan ya wallafa karin bayani a kan lamarin da cewa, “Na dauki aniyar ci gaba da yakar APC ta da da kuma manufofinta, zan kuma ci gaba da yakar ta har karshen rayuwata.”
Amma da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels, Fani-Kayode ya bayyana cewa APC ta yanzu ta sha bambam a shugabanci da APC ta baya.
A cewarsa, da ba a canza shugabancin jam’iyyar ba, babu dalilin da zai sa ya koma cikin ta.
Ya ce, “Abubuwa da yawa sun faru a cikin APC cikin shekara biyu da suka gabata. Za ku yarda da ni? Kai mai sharhin siyasa ne.
“Kun san abin da ya faru a APC, kun san abin da ya faru a PDP, ba zan yi magana game da PDP a nan ba har sai ta tanka min, sannan zan ba da amsa.
“APC da nake magana a wancan lokacin ba ita ce APC a yau ba. Shugabancin APC na wancan lokacin ba shi ne yake aiki a yanzu ba.
“A yau idan ka duba shugaban rikon kwarya na yanzu, Gwamna Mai Mala Buni, ya yi kokari wajen dinke matsalolin jam’iyyar wanda hakan na da bambamcin da kafin yanzu.
“Tsohuwar APC daban ce, wadda da ba a sauya shugabancinta ba babu abin da zai sa na shigo cikinta. Yanzu kuwa APC tana da tsarin sauraren jama“a tare da kawo gyara da karbar koken jama’a,” inji Kayode.