✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Legas

APC ta samu nasara a kujeru 375 daga cikin 376 na kansiloli a fadin jihar, inda jam’iyyar PDP ta samu kujera guda daya a mazabar…

Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkan kujerun shugabancin ƙananan hukumomi guda 30 a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a Jihar Legas.

Shugabar Hukumar ta (LASIEC), Mai Shari’a Bola Okikiolu-Ighile (mai ritaya) ce ta bayyana hakan yayin sanar da sakamakon zaben a wajen taron ’yan jarida a Sakatariyar Hukumar da ke Yaba a ranar Lahadi.

Ta bayyana cewa jamiyyar APC ta kuma samu nasara a kujeru 375 daga cikin 376 na kansiloli a fadin jihar, inda jam’iyyar PDP ta samu kujera guda daya a mazabar Ward D a Yaba.

Shugabar hukumar zaben ta kuma bayyana farin ciki dangane da yadda aka gudanar da zaben lami lafiya.

Sai dai bayanai sun ce jam’iyyun adawa na PDP da APP sun yi watsi da sakamakon zaben wanda aka gudanar a ranar Asabar.

Da yake jawabi, Shugaban kungiyar ’yan Arewa magoya bayan jam’iyyar APC a mazavar raya karkara (LCDA) ta Yaba, Kwamared Ghali Sulaiman Kabiru ’Yanleman, ya shaida wa Aminiya cewa “ka san cewa siyasar Kudancin Nijeriya musamman ma a Jihar Legas ba za ta yiwu ba sai an tafi tare da ’yan Arewa saboda yawan mutanenmu da ke zaune a sassa daban-daban na wannan yanki da kwarewa da irin rawar gani da muke takawa a harkokin siyasa.

Hakan ne ya sa shugabannin jam’iyun siyasa suka yanke shawarar ‘yan Arewa sun cancanci samun wakici a kowace mazaba da kananan hukumomi da suka tabbatar da nada Alhaji Sa’adu Gulma Dandare a matsayin Shugaban Kungiyar ‘yan Arewa magoya bayan jam’iyyar APC a Jihar Legas da Kudancin kasa baki daya.”