Jam’iyyar APC ta bukaci Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da ’yan sanda da su kubutar da Sanata Nelson Effiong da aka yi garkuwa da shi cikin koshin lafiya.
An yi garkuwa da Sanata Nelson Effiong ne a ranar Lahadi a garin Uyo, babban birnin Jiharsa ta Akwa Ibom.
Ko da yake kawo yanzu masu garkuwa da shi ba su tuntubi iyalansa ba, “Shugaban Kwamitin Rikon na APC a Jihar Akwa Ibom, Dokta Ita Udosen, a madadin jam’iyyar yana kira ga hukumar DSS da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar da su gaggauta daukar matakin kubutar da shi ya koma ga iyalansa cikin koshin lafiya tare da hukunta wadanda suka aikata laifin.
“Jam’iyyar na kuma kira ga iyalan Sanata Effiong da ma sauran jama’a da su ba da gudunmawa da bayanan da za su taimaka wa jami’an tsaro su kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da shi cikin koshin lafiya.
“Sannan jam’iyyarmu za ta yi duk abin da za ta iya na tabbatar da ganin an sako Sanata Effiong, tana kuma kira ga ’yan jam’iyya da su sanya shi a cikin addu’o’insu domin ya dawo ga iyalansa cikin koshin lafiya”.
Sanarwar da Sakataren Yada Labaran APC a Jihar, Nkereuwem Enyongekere, ya fitar a ranar Talata ta kara da cewa, “Jami’yyarmu ta girgiza da samun labarin garkuwa da Sanata Nelson Effiong, wanda daya ne daga cikin shugabannin jam’iyya kuma tsohon Sanata mai wakilatar Kudancin Akwa Ibom a Majalisar Dattawa.”
Sanata Effion shi ne kadai dan jam’iyyar APC a cikin sanatocin da suka wakilci Jihar Akwa Ibom a Majalisar Dattawa ta takwas da wa’adinta ya kare a shekarar 2019.