Shugaban Kwamitin riko na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya ce jam’iyyarsu ta tsara yadda za ta ci gaba da zama a karagar mulkin kasar har na tsawon shekara 32.
Mai Mala wanda ke zaman Gwamnan Jihar Yobe, ya bayyana hakan ne a Hedikwatar jam’iyyar da ke birnin Abuja, inda ya ce matukar jam’iyyar ta samu wannan dama ta jagorancin kasar a tsawon wa’adi takwas rigis, to kuwa za ta inganta rayuwar al’umma fiye da yadda aka zata.
- ‘Ana fakewa da sunan rikicin Makiyaya don a raba kan Arewa’
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 2 a Sakkwato
Furucin gwamnan na zuwa ne yayin kaddamar da kwamitin tuntuba da tsare-tsare na jam’iyyar karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa.
Aminiya ta samu cewa, jam’iyyar ta kaddamar da wannan kwamiti mai mutum 61 domin kammala duk wani shiri gabanin babban taron da za ta yi a watan Yunin bana.
“Manufar kafa wannan kwamiti na tuntuba da tsare-tsare shi ne tabbatar da jam’iyyar ta cimma burinta na kawo managarcin sauyi a kasar nan.”
“Burinmu shi ne tsayuwa a kan tafarkin da zai ba mu damar aiwatar da dukkanin manufofin jam’iyyar da kuma inganta rayuwar al’umma,” in ji Buni.
Buni ya kara da cewa, jam’iyyar tana bukatar ta ci gaba da kasancewa a karagar mulki domin tabbatar da dorewar tsarin dimokuradiyya da ta dora kasar a kai tun hawanta mulki a shekarar 2015.
A nasa bangare, Gwamna Badaru ya ce Kwamitin rikon ya jajirce wajen ganin ya yi wa jam’iyyar matashiya da tsare-tsare da za su kai ta ga ci.
Kazalika, Gwamna Badaru ya ce a halin yanzu jam’iyyar ta yi wa mambobi miliyan 36 rajista yayin sabunta rajistar ’ya’yanta da ke ci gaba da gudana wanda za a kammala a ranar 31 ga watan Maris.