✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Yobe za ta gina gadar sama a kan N22.3bn

Gwamnatin ta jaddada aniyarga ta ci gaba da samar wa al'ummar jihar ababen more rayuwa.

Gwamnatin Jihar Yobe, ta rattaba hannu kan kwangilar gina gadar sama da titin ƙarƙashin ƙasa a tsakiyar garin Damaturu, Babban Birnin Jihar, kan kuɗi Naira biliyan 22.3.

Wannan wani mataki ne na ci gaba a ƙoƙarin gwamnatin samar wa al’umma ababen more rayuwa.

Kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Umar Duddaye ne, ya sanya hannu a madadin gwamnati, yayin da Injiniya Habib Geojea ya wakilci kamfanin da zai aiwatar da aikin, Messrs Triacta Nigeria Limited.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin Mai Mala Buni na bai wa manyan ayyukan ci gaba fifiko, wanda ya haɗa da tituna, gadoji, da magudanun ruwa.

Ya ce aikin gadar sama da ke shatale-shatalen Damaturu za a kammala shi cikin watanni 12.

Haka nan, an rattaba hannu kan kwangilar gina titin Damaturu zuwa Gambir tsakanin gwamnatin Yobe da kamfanin Messrs Elegance Construction Nigeria Limited, wanda za a kammala cikin watanni tara.

Kwamishinan ya ƙara da cewa ana shirin gina sabbin tituna masu tsawon kilomita 23.5 da magudanan ruwa masu nisan kilomita 27 a Damaturu, tare da sake da gyara titunan da ake buƙata.

Aikin zai shiga mataki na biyu a shekarar 2025.

Manajan yanki naTriacta Nigeria Limited ya tabbatar da cewa za su gudanar da aikin cikin inganci da wa’adin da aka tsara.