Agboola, wanda yake jawabi jim kadan ya kada kuri’arsa a akwati mai lamba 004, mazabar Apoi a Karamar Hukumar Kiribo Ese-Odo ya bayyana rashin gamsuwarsa da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da sauran jami’an tsaro game da magudin da yake zargi.
- Zaben Ondo: Dan takarar PDP ya koka kan matsalar na’urar tantance masu zabe
- An rufe hanya saboda zaben Gwamnan Ondo
“Na lura mutane da dama sun fito zaben kamar yadda ya kamata, amma maganar gaskiya ban gamsu da yadda na ga tsarin yadda ake tafiyar da harkar tsaro ba, akwai hadin baki.
“Muna kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da zama ‘yan ba-ruwanmu ta hanyar tabbatar da cewa babu wani mai zaben da aka tauye wa hakkinsa.
“Dazun nan nake samun labari cewa wani babban dan ta’adda a kasar nan wanda ba ma dan yankin ba ne shi da tawagarsa sun yi wa yankin kawanya suna tilasta wa masu zabe su zabi jam’iyyar APC, alhali jami’an tsaro na wurin suna kallon su.
“Saboda haka ina kira ga Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya da ya tsawatar a lamarin domin rashin adalci ne da kuma kauyanci.
“Kamata ya yi a kyale mutane su zabi abin da suke so ba tare da musgunawa ba,” inji Agboola.