✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ce ta kawo rabuwar kai a Najeriya —Atiku

Ba mu taba ganin irin rashin hadin kan da muke fama da shi a kasar nan ba, ko da a lokacin yakin basasa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, kuma mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce Najeriya ta samu rabuwar kai saboda rashin adalci da gwamnatin APC ta yi wa wasu sassan kasar nan.

Atiku ya jadaddacewa ko a lokacin yakin basasa Najeriya ba ta wargaje ba kamar yadda ake gani a lokacin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Atiku ya  bayyana hakan ne a ranar Asabar a garin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, yayin da ya ke jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP gabanin zaben fidda-gwani na shugaban kasa.

Wazirin Adamawa, ya ta’allaka kalubalen rashin tsaro da ke barazana ga zaman lafiyar Najeriya ga rashin yin katabus da Buhari ya yi.

A cewarsa, muddin kasar nan ba ta hade ba, muddin babu zaman lafiya, ba za ka iya gudanar da mulki ko da a gidanka ba ne, duk sa cewar Najeriya kasa ce mai kabilu da addinai daban-daban .

Ya yi alkawarin hada kan Najeriya ta hanyar bai wa kowane bangare dama da adalci, magance matsalar rashin tsaro da aiwatar da tsarin bunkasa tattalin arzikin kasar nan domin kawo sauyi.

Atiku ya kuma jadadda alkawarinsa na kwace iko daga hannun gwamnatocin jihohi zuwa kananan hukumomi don ba su damar cin gashin kansu.

Ya kuma ba da tabbacin cewa ba zai bai wa ‘yan Najeriya kunya ba idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023 ba.

“Ba mu taba ganin irin rashin hadin kan da muke fama da shi a kasar nan ba, ko da a lokacin yakin basasa… kuma me ya sa muka samu rabuwar kai, saboda gwamnatin APC ba ta yi adalci a dukkan sassan kasar nan ba.

“Na yi alkawarin hada kan kasar nan, na yi alkawarin ba da dama ga kowane bangare na kasar nan, mun taba yin hakan a baya a 1999 lokacin da muka hau mulki, an samu rarrabuwar kai da yawa amma abin bai kai na yanzu ba.

“Amma abu na farko da muka yi shi ne mun tabbatar mun kafa gwamnatin hadin kan kasa kuma hakan ya ba mu kwanciyar hankali da hadin kan da ya kamata mu yi mulki.

“Matukar kasar nan ba ta hade ba, muddin babu zaman lafiya ba za ka iya mulkin ko da a gidanka ba ne, don haka na yi alkawarin bayar da dama ga kowane bangare na kasar nan.

“Kwanakin baya wani gwamna ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban kasa, inda ya ke maganar bai wa kananan hukumomi damar cin gashin kai, amma abun mamaki a halin yanzu a jiharsa ya gaza bai wa kananan hukumomin wannan ‘yancin cin gashin kan.

“Don haka wannan yana daya daga cikin  munafurcin wasu shugabanninmu ke yi.  Shi ya sa na ce tsarin mulkin za mu fara kawo wa gyara, ta yadda kananan hukumomin za su samu ‘yancin gashin kansu.

“Idan kuka zabe ni, na yi alkawari ba zan baku kunya ba, kuma ba zan bai wa Najeriya kunya ba.”

Shi ma a nasa jawabin, wani dan takarar gwamna a jihar, Oladipopu Adebutu, ya koka kan matsalar tsaro, rashin ayyukan yi da kuma talauci da ya addabi al’ummar kasar nan.

Sai dai ya ce babbar jam’iyyar adawa [PDP] tana kan hanyar sake kwace mulki a Jihar Ogun da Najeriya baki daya.

Daga cikin tawagar da suka yi wa Atiku rakiya akwai; Raymond Dokpesi, Sanata Dino Melaye da sauran mambobin jam’iyyar PDP.