Tsohon Firayi Ministan kasar Portugal Mista Antonio Guterres ne sabon Sakatare-Janar na Majalisar dinkin Duniya.
A jiya Alhamis ce Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniyar ya kada kuri’ar tabbatar da mukamin ga Mista Guterres, wanda ya jagoranci Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar dinkin Duniya na tsawon shekara 10 don maye gurbin Mista Ban Ki-Moon a badi.
Mambobin Kwamitin Sulhun 15 sun kada kuri’unsu a boye ga masu takarar su 10 a ranar Laraba, kuma babu wanda bai amince da Mista Guterres ba.
A shekaranjiya Laraba ce Jakadan kasar Rasha a Majalisar dinkin Duniya Mista bitaly Churkin, ya sanar da cewa Mista Guterres, mai shekara 66 a duniya aka fi so.
Mista Guterres wanda Injiniya ne ya fara shiga harkokin siyasa ne a zaben dimokuradiyya na farko a kasar Portugal a 1976 bayan juyin da ya kawo karshin mulkin sarakuna na shekara 50. Tauraronsa ya haskaka cikin sauri har ya zama jagoran Jam’iyyar Socialist a 1992 sannan aka zabe shi Firayi Minista a 1995.
“Mutane sun yi ittifaki kan wani mutum wanda ya burge kowa a daukacin zaman,” inji shi.
Jakadan Ingila Majalisar Matthew Rycroft ya ce Mista Guterres “Zai kai Majalisar dinkin Duniya zuwa mataki na gaba wajen kyakkyawan shugabanci kuma ya zamo yana da tagomashi a idon duniya a daidai lokacin da duniya ta samu rarrabuwar kai kan wasu al’amura.”
An sa ran a wannan karo a zabi mace a kan mukamin, inda mata bakwai da suka hada da Irina Bokoba mai shekara 63 ’yar kasar Bulgeriya kuma Darakta Janar ta Hukumar UNESCO da Helen Clark mai shekara 66 tsohuwar Firayi Ministan kasar New Zealand kuma shugabar Hukumar UNDP da Natalia Gherman mai shekara 47, ’yar siyasar Moldoba kuma Mataimakiyar Firayi Minista kuma Ministar Hade kasashen Turai daga shekarar 2013-2016.
Saura su ne Misis besna Pusic mai shekara 62, Shugabar Jam’iyyar Croatian People’s Party da ta rike mukamai da dama a kasarta da Kristalina Georgieba mai shekara 63, Kwamishinar Kasafin Kudi da Kula da Ma’aikata ta Tarayyar Turai da ’yar kasar Sabiya buk Jeremic da kuma ’yar kasar Slobakia Misis Miroslab Lajcak.
Antonio Guterres ne sabon Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya
Tsohon Firayi Ministan kasar Portugal Mista Antonio Guterres ne sabon Sakatare-Janar na Majalisar dinkin Duniya.A jiya Alhamis ce Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniyar ya…