✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Annan ya bukaci sojoji su mutunta hakkin Musulmin Rohingya

Tsohon Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya, Mista Kofi Annan ya bukaci sojojin kasar Myanmar (Burma) su rika gudanar da harkokinsu bisa doka a yayin…

Tsohon Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya, Mista Kofi Annan ya bukaci sojojin kasar Myanmar (Burma) su rika gudanar da harkokinsu bisa doka a yayin gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Yamma na kasar, inda sojojin suka kai hare-hare tare da kashe akalla Musulmi 86 kuma suka tilasta fiye da dubu 10 yin gudun hijira zuwa iyakar kasar Bangladesh.

Rikicin shi ne kalubale mafi girma da gwamnatin Misis Aung San Suu Kyi mai wata takwas take fuskanta, kuma hakan ne ya sanya ake ta kiraye-kiraye gare ta ta kara zage dantse wajen taimaka wa Musulmin Rohingya marasa rinjaye, wadanda aka hana wa izinin zama ’yan kasa ko samu kayayyakin bukatun rayuwa.
Annan wanda yake jagorantar wata hukuma da gwamnatin kasar ta kafa don samo maslaha kan rikicin da ke tsakanin mabiya addinin Buddah masu rinjaye da Musulmin Rohingya ya ce bai kamata jami’an tsaro su rika tozarta hakkin jama’a ba.
“Babu sabani a tsakanin tsaro da hakkin jama’a,” ya shaida wa manema labarai a Yangon, birnin kasuwanci bayan ya gana da Suu Kyi da kuma Babban Kwamandan Askarawan kasar, Min Aung Hlaing lokacin da ya ziyarci kasar a karo na biyu.
Ya ce “A duk lokacin da ake gudanar da aikin tsaro wajibi ne a kare fararen hula a kowane lokaci, don haka ina kira ga hukumomin tsaro su rika gudanar da aiki tare da cikakkiyar biyayya ga doka.”
Annan ya ce kwamitin “Ya damu sosai kan rahotannin zargin keta hakkin jama’a da ake yi.”
Sai dai mahukuntan Myanmar sun yi watsi da zargin da mazauna yankin da kungiyoyin kare hakkin jama’a na cewa sojoji sun yi fyade ga mata Musulmi na Rohigya tare da kone gidaje da kuma kashe fararen hula a lokacin da suka kai mamaya don mayar da martani kan hare-haren da aka kai a kan iyakar kasar da kasar Bangladesh.
An gudanar da zanga-zanga a kasashen Asiya, musamman a Indonusiya da Malesiya da Bangaladesh, inda fiye da mutum dubu 10 suka yi zanga-zanga a ranar Talatar da ta gabata a wajen ofishin jakadancin kasar Myanmar da ke Dhaka, babban birnin Bangladesh don la’antar cin zarafin Musulmin Rohingya da ake yi, kamar yadda wani dan sandan birnin ya shaida wa Reuters.
Wani jami’in Majalisar dinkin Duniya ya ce fiye da Musulmi dubu 10 ne suka yi hijira zuwa Bangladesh daga Myanmar a ’yan makonnin nan.