Wani mutum ya kaurace wa budurwar da zai aura a ranar aurensu, bayan da iyayen amaryar suka gaza samar da naman tunkiya ga masu halartar bikin aurensu.
Kafar labarai ta The New Indian Express, ta ce, angon mai shekara 27 mai suna Ramakant Patra, daga baya ya auri wata mata a yankin kafin ya koma gida.
- Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 5 a Indiya
- Iska mai karfi ta kashe mutum 2 ta rushe gidaje 1,500 a Katsina
Patra, mazaunin garin Rebanapalaspal da ke kusa da Gundumar Keonjhart, ya je kauyen Bandhagaon da yake yankin Sukinda tare da dangin ango da niyyar aure a yammacin ranar Larabar karshen watan jiya.
Kuma yana isa wurin daurin auren iyalan budurwar suka yi masa maraba, inda bayan kammala al’adun da suka kamata, sai aka dunguma wajen cin abinci.
Sai dai kafin a kawo abinci, sai mahalarta daurin auren suka bukaci a kawo naman tunkiya da ya sha kori.
Sai dai kuma iyalan amarya ba su dafa ba, don haka dangin ango suka fara muhawar da dangin amarya da suke rarraba abincin.
A karshe lamarin ya kazance inda aka fara dambacewa inda bayan Patra yana gano cewa ba a kawo dafaffen naman tunkiya don walimar auren ba, ya ce ya fasa auren lamarin da ya ba kowa mamaki.
Iyalan amaryar sun yi ta ba shi hakuri suna lallashinsa kan ya canja tunaninsa, amma haka ya shuri takalmansa ya yi gaba shi da danginsa.
Daga nan sai Patra ya tafi gidan wadansu ’yan uwansa a kauyen Gandhapala a yankin Kuhika a Sukinda inda suka wuni.
Daga baya sai ya auri wata mace a Phulajhara da ke yankin Tamka a daren ranar inda ya koma kauyensu na Keonjhar, kamar yadda wata majiya ta tabbatar.
Babu wanda ya kai kara ga ’yan sandan yankin kan wannan mataki, alhali a shekarun 1980 ana kai rahoton irin wannan lamari na angon.