Ana zargin wani matashi mai suna Usman Adamu Aliyu mai shekara 19 da yunkurin hallaka wadansu almajirai biyu da nufin sayar da kawunansu a garin Bauchi.
Shugaban kungiyar Sintiri ta Garu Security Guards ta Jihar Bauchi, Malam Dawa Ya’u Felu, wadda jami’anta suka yi nasarar kama wanda ake zargin ya shaida wa manema labarai a Bauchi cewa, “Almajiran biyu, masu suna Hassan Usman mai shekara 11 da Sa’idu Muhammad mai shekara 10, mazauna Unguwar Ibrahim Bako ne da ke hanyar Gombe a Bauchi, inda suke almajiranci a hannun Malam Umar Muhammad Ladan, kuma wanda ake zargin ya yaudare su ne zuwa madatsar ruwa ta Gubi, inda ya yi niyyar kashe yaran.
Malam Dawa Felu ya ce bayan ya kai su ne wani manomi ya ga daya daga cikinsu yana gudu yana neman dauki yana cewa ga wani zai kashe shi, shi kuma sai ya kai rahoton lamarin ga Sarkin Firo, “aka kira mu, isarmu wurin ke da wuya muka samu manomin ya yi kukan kura ya kama matashin,” inji Dawa Felu.
Shugaban ya ce bayan da suka kama matashin sai suka kai shi ofishinmu don gudanar da bincike inda matashin ya amsa cewa ya so hallaka yaran ne. Sai dai ya ce yaron ya yi masa rashin kunya ne, inda ya samu wani abokinsa sai shi abokin nasa mai suna Mubarak ya ce masa, dama yana son sassan jikin mutane. Ya ce ya saba ko ya jefa mutum a ruwa ko ya cire sassan jikin mutum. Don haka ya je kawai ya ciro masa kan yaron domin ya huce haushi. Sai dai ya ce bai san me abokin nasa zai yi da kan yaron ba in ya ba shi.
“daya daga cikin almajiran, Sa’idu Muhammad ya ce ya yi kururuwar neman taimako ne, lokacin da ya ga an maka wa dan uwansa dutse a tsakiyar kansa. Al’amarin da ya janyo hankalin jama’a daga wani bangare na madatsar ruwan ta Gubi suka kai wa almajiran gudummawa,” inji Malam Dawa.
Ya ce, sun yi dabara wajen tabbatar da kamo wanda ake zargi sun shirya kashe yaran da shi. “Mun sanya ya kira Mubarak din wani mazaunin Unguwar Kandahar a nan Bauchi, inda ya shaida masa cewa ya kammala aiki, sai wanda ya sa shi aikin, ya ce masa yanzu ya yi nisa don haka ya boye masa kan yaran idan ya dawo zai amsa. Mun yi dabara ba mu ce masa ya nuna mun kama shi ba, sai Mubarak din ya ce da Usman ya ajiye masa kan zuwa gobe.”
Ya ce a yanzu haka sun mika wadanda ake tuhuma ga ’yan sanda, domin gudanar da bincike.
Malamin almajiran Alaramma Umar Muhammad, ya ce almajiran nasa sukan dan gudanar da aikace-aikace a gidan su wanda ake zargi, domin neman na abinci kafin lamarin ya faru.
Malamin ya ce, Usman Adamu, kamar yadda ya yi ikirari yana zargin Sa’idu ne da yi masa kazafin satar ragon mahaifinsa, ya tafi da shi wani wurin da ba a fayyace ba ya sayar, wanda wannan kazafi ya bata masa rai. Amma mun sasanta su har na tambaye shi ya hakura, ya ce, ‘eh,’ ya kuma ce gobe yaran su zo zai ba su kayan sanyawa.
Malam Umar ya ce, “Bayan yaran sun tashi karatun safe, sukan tafi neman dan abin da za su kai baka, kuma bisa al’ada sukan dawo makaranta a kan lokaci, amma da maraice ta yi ba mu ga yaran ba; shi ne na sa wadansu yaranmu su dudduba su ko za su gansu ba a gan su ba sai zuwa Magariba aka buga min waya, aka shaida min halin da almairan biyun su ke ciki.”
Ya ce, yana da almajirai kimanin 150 da suke karatu a karkashinsa, kuma ya ce suna gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba, sai ya bukaci jami’an tsaro su tabbatar da an yi kyakykywan bincike an kuma hukunta wanda ya aikata laifin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, Kamal Datti Abubakar ya shaida wa Aminiya cewa yana ci gaba da tattara bayanai kan wannan lamari, inda ya bukaci ta ba shi lokaci.