✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin matashi da sace mazakutan samari 5 a Jigawa

Wannan shi ne karon farko da na aikata wannan ta’asa da ta yi sanadiyyar shiga ta hannu.

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens, ta cafke wani matashi mai shekaru 24 da ake zargi da sace mazakutan wasu samari biyar a Karamar Hukumar Dutse ta Jihar Jigawa.

Kakakin hukumar, ASC Badrudeen Tijjani Mahmud ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis.

A cewarsa, matashin da ake zargi ya fito ne daga kauyen ’Yan Ciyawa na Karamar Hukumar Nguru ta Jihar Yobe.

Ya ce a ranar Litinin 29 ga watan Janairu ne suka kama matashin kan zargin sace mazakutan wasu samari biyar a unguwar Gida Dubu da ke birnin Dutse.

ASC Badrudeen ya ce ana zargin ya sace mazakutan samarin — Yusuf Musa, Abubakar Faruq, Ibrahim Abubakar, Jamilu Nasiru da Abdulmumin Nura — wadanda suka kai korafi babban ofishinsu da ke Dutse.

Da yake amsa tambayoyi, matashin ya ce ya shiga wannan harkalla ce bayan haɗuwa da wani mutumi da ko saninsa bai yi ba yana tsakar tafiya a daidai Babban Shataletalen da ke garin Nguru.

“Mutumin ya shaida min cewa yana neman wanda zai riƙa taimaka masa wajen satar mazakutan jama’a, kuma ya haɗa ni da naira 20,000 domin mu ƙulla yarjejeniya.

“Gaskiya saboda ina cikin matsananciyar bukatar kuɗin ya sanya na karɓa amma ba ni da masaniya kan abin da zai yi da mazakutan idan ya samu,” a cewar matashin da ake zargi.

Aminiya ta ruwaito cewa, matashin ya tabbatar da sace mazakutan samarin da suka kai korafi amma tuni ya dawo musu da kayansu bayan ya shiga hannu.

Sai dai matashin ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko da ya aikata wannan ta’asa da a sanadiyyar hakan aka kama shi.

Kwamandan Hukumar Sibil Difens a Jihar Jigawa, Muhammad Danjuma, ya ba da umarnin faɗaɗa bincike a kan lamarin, wanda daga bisani za a gurfanar da matashin da ake zargi a gaban kuliya.