✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin matashi da kashe ’yar yayansa da binne ta a tsaye

Wasu dai na zargin watakila Tsafi ya yi da ita saboda yadda ya binne ta a tsaye

Ana zargin wani matashi mai kimanin shekara 30 da sace ’yar yayar shi mai shekara 11 a duniya daga Zariya, sannan ya kashe ta tare da binne ta a tsaye a gidansa da ke Kano.

Wanda Ake zargin, mai suna Jafar Sidi Gambo mazaunin unguwar Karauka Bakin Kasuwa ne cikin Birnin Zariya, kuma kani ne ga mahaifiyar yarinyar mai suna Amina Salisu Sani Mai Mai.

Da yake zantawa da jaridar Aminiya, mahaifin yarinyar ya ce an sace ’yar tashi ne tun ana saura kwana biyar Sallah Karama.

Mahaifin ya kara da cewa sai dai ba a gano ta ba sai a ranar Laraba a garin Kano, a gidan kawun nata inda ya binne gawar ta bayan ya kasheta.

Ya ce, “Shi Jafar ne ya dinga kiran waya cewa Amina ta zo gidan kakanninta domin zai saya masu wani abu. Da ta je bayan wayewar gari sai aka nemi Amina aka rasa.

“Da aka tabbatar ba ta nan, shi ne yayanta wanda ke da shagon dinki kusa da gidan, ya tuno cewa, Amina ta shigo shagon su inda take gaya mishi cewa zasu tafi Kano da kawu Jafar amma ya ce kada ta gaya wa kowa.

“Daga nan ne muka kira shi a waya inda ya musanta cewa yana tare da marigayiyar. Hakan ya sa na tafi ofishin ’yan sanda inda na shigar da kara,” inji shi.

Mahaifin yarinyar yabce bayan binciken ’yan sanda, wanda ake zargin ya tabbatar da cewa shi ne ya dauki marigayiya Amina kuma daga baya ya halaka ta.

A cewar shi, bayan an je gidan da aka binne yarinyar a layin Malfa da ke unguwar Kofar Wambai a Kano inda a can yake zaune da iyalinsa, Jafar ya nuna wani tsohon dakin girki inda aka haka kuma aka zakulo gawar yarinyar.

“Sai dai abin da ya fi tsaya min a rai shi ne, gawar a tsaye aka binne ta ba a kwance ba kamar yadda ake yi wa mamaci,” inji mahaifin yarinyar.

Sai dai ra’ayin mutane ya sha banban akan kisan Amina da irin wanda ya faru a garin Kano da Bauchi, kasancewar ita wannan ba a nemi biyan kudin fansa ba, da kuma yadda aka binne gawar a tsaye dan haka ake zaton nashi kamar tsafi ne ya yi da ’yar yayan ta shi.

Wadda ake zargin yana hannun jami’an ’yan sanda da ke babban ofishin shiya ta daya a Zariya.

Sai dai da aka tuntubi mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya ce har yanzu maganar ba ta je wurinsu ba tukunna.