✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin matasa 3 da satar ’yar shekara 6 a Katsina

Matasan sun sace yarinyar a Kano tare da boye ta a Jihar Katsina.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wasu matasa uku da ake zargi da sace wata yarinya ‘yar shekara uku kacal a duniya.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ne ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Laraba.

A cewarsa, matasan uku da ake zargi duk cikinsu babu wanda ya wuce shekara 19 a duniya.

Kakakin ya ce matasan sun hada baki wajen sace karamar yarinyar a unguwar Bachirawa da ke Jihar Kano a ranar 6 ga watan Janairu, 2023.

Isah ya ce sun dauke yarinyar zuwa Katsina inda suka bukaci iyayenta su biya kudin fansa Naira miliyan biyu.

“Muna samu rahoton faruwar lamarin muka shiga bincike, kuma mun yi nasarar kama wani daya daga cikin wadanda ake zargin.

“A yayin bincike ne muka gano inda aka boye wadda lamarin ya shafa.

­“Mun ceto yarinyar sannan mun kama wadanda suka sace ta.”

Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar sun kammala bincike.