An maka Mai Unguwar Dangulam da ke Karamar Hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa a kotu kan zargin aikata fyade da kuma sanya wa wata karamar yarinya kwayar cutar HIV.
Wata takarda da Ma’aikatar Shari’a ta jihar ta aike wa Sakataren Masarautar Dutse, ta ce yarinyar da mahaifinta suna zargin ta dauki juna biyu a sakamakon fyaden da mai unguwar ya yi mata.
Wasikar da ta bukaci majalisar masarautar ta ce, “Nan gaba za a gurfanar da mai unguwar Dan Gulam kan zargin da wani magidanci ya kawo wa Antoni-Janar cewa basaraken ya yi wa ’yarsa fyade dauki ciki kuma ya sa mata kwayar cutar HIV.”
Don haka ta bukaci Majalisar Masarautar Dutse ta dauki matakin da ya dace gabanin gurfanar da wanda ake zargin a matsayin basarake.
- An kama tsohon shugaban mulkin sojan Guinea da ya tsere daga gidan yari
- Masarautar Adamawa ta tube Hakimin Ribadu
Wasikar, dauke da sa hannun Kabiru Abdullah Esq, ta ce bayan samun korafin ne Antoni-Janar na jihar ya bukaci ’yan sanda su gudanar da bincike kan lamarin.
Da farko wanda ake zargin ya shaida wa ’yan sanda cewa ya yi karar yarinyar da mahaifinta a Babbar Kotun Musulunci da ke Gwaram bisa zargin zubar masa da kima.
Da jin haka ne kwamihinan shari’ar ya bukaci a dawo da lamarin gabansa, inda ya kara umartar sashen binciken manyan laifuka na ’yan sanda su binciki duka bangarorin da ke rikicin.
Wasikar ta ce, bayan bincike ’yan sanda suka tabbatar da zargin da ake wa mai unguwar, shi ne, “Antoni-Janar ya sa in sanar da Mai Martaba, don guje wa gurfanar da wanda ake zargin a matsayin basarake a masarautar.”
Iyayen yarinyar dai na rokon kungiyoyin kare hakki da su sanya baki cikin lamarin domin ceto rayuwarta da kuma sama mata adalci.