✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana Zargin Firinsifal Da Cin Zarafin Dalibarsa A Katsina

Gwamnatin Katsina ya dakatar da shugaban makarantar nan take bisa zargin cin zarafin ɗalibarsa

Ana zargin shugaban wata makarantar sakandaren je-ka-ka-dawo a Jihar Katsina da cin zarafin wata ɗalibarsa.

Wannan dambarwa dai ta kunno kai ne a makarantar sakandaren gwamnati da ke Dantankari da ke Karamar Hukumar Dandume ta jihar.

Gwamnan jihar, Umar Dikko ya umarci ya umarci kwamishinan ilimin bai-ɗaya na jihar da ya dakatar da shugaban makarantar nan take.

Sanarwar da kakakin gwamnan, Abdullahi Aliyu Yar’Adua ta kuma umarci kwamishinan ilimin ya binciki lamarin, ya dauki matakin da ya dace, sannan ya kai wa gwamnan rahoro.

Gwamnatin jihar ta kuma umarci Kwamishinan ’Yan sandan jihar ta ya binciki zargin da ake yi wa malamin.

Har ila yau, ya binciki jami’in ’yan sanda (DPO) na karamar hukumar ta Dandume a kan zargin neman a yi sulhu kan lamarin a lokacin da aka kai mashi koke, shi ma a kai rahoto ga gwamna.