Jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Muhammad, wadda aka fi sani da Maryam Malika, ta bayyana damuwa ga me da yadda mutane da dama ke musu wa bakin fenti da cewa jarumai mata a masana’antar ba sa zaman aure.
Jarumar ta bayyana haka ne cikin ‘Daga Bakin Mai Ita’ na Sashen Hausa na BBC.
- Kotu ta yi watsi da bukatar belin Sheikh Abduljabbar
- Mahara sun kashe mutum 50, sun kona gidaje a Neja
“Duk burin wata ’ya mace ita da iyayenta bai wuce ta samu miji ta yi aure ba.
“A lokacin da nake harkar fim Allah Ya kawo min miji na yi aure, muka je na zauna sai ga kuma kaddara wadda ta riga fata, shi ne ya ba ni damar da na sake dawowa harkar fim.
“Yanzu ba ni da wani buri wanda ya wuce Allah Ya fito min da miji na yi aure,” a cewar Malika.
– Malika ta nuna rashin jin dadinta
Sai dai jarumar ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda wasu mutane ke cewa matan Kannywood ba sa zaman aure.
“Gaskiya ba na jin dadi kuma raina yana baci sosai saboda suna nuna kamar cewa ba su san kaddara ba.
“Ka san dama mu ’yan fim ana cewa ba sa zaman aure, to ba haka ba ne, duk wadda ka ga ta fito daga gidan mijinta kaddara ce, babu macen da za ta so ta yi aure ta fito.
“Ina so mutane su fahimta su san cewa don Allah su daina yada jita-jita a kan abin da ba su gani ba kuma ba su tabbatar ba, idan hakan ta faru ba ma bukatar komai idan ba addu’a ba,” in ji ta.
Jarumar ta ce tsakanin ’yan kallo da su addu’a ce ta kamata ta shiga tsakaninsu ba ka-ce-na-ce ba.