Zanga-zangar adawa da manufofin kasashen yamma da ke gudana a Nijar da juyin mulki a Burkina Faso na ci gaba da haifar da shakku kan ayyukan sojojin Jamus a yankin Sahel.
Koda yake ana samu ‘yan siyasan kasar Jamus da ke da ra’ayin ci gaba da gudanar da aikin rundunar Bundeswehr a kasashen yammacin Afirka.
- DAGA LARABA: Tattaunawa Ta Musamman Da Shugaban Hukumar INEC
- Ya kamata ’yan Najeriya su manta da kura-kuran mulkin PDP —Adetokunbo
‘Yar Majalisar Tarayyar Jamus, Sevim Dagdelen ta yi la’akari da irin abubuwan da ke faruwa a Mali da makwabtanta na kasashen Sahel wajen bayyana matsayi mai tsauri kan zaman sojojin kasarta a yankin.
Hasali ma shugabar sashin kula da huldar kasa-da-kasa da tsaro a Jam’iyyar Die Linke ta nuna bukatar janye sojojin Jamus a Mali.
Sai dai majalisar dokoki ta Bundestag ta gindaya sharudan yin aiki kafada-da-kafada da tawagar kiyaye da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali wajen tsawaita wa’adin Bundeswehr.
Kudurin ya ba da damar yin taka tsantsan wajen daukar matakan da suka dace bisa la’akari da halin da ake ciki na juye-juyen mulki a Mali da Burkina Faso.
Wannan ne ya sa kusoshin jam’iyyun SPD da FDP ke kira da a kawo karshen ayyukan rundunar kawancen gwamnatin Jamus a Mali cikin gaggawa.
Sai dai Agnieszka Brugger, Mataimakiyar Shugabar Jam’iyyar The Greens a Bundestag, tana adawa da janye sojojin Jamus a Mali, tana mai cewa dole ne a yi sara ana duban bakin gatari, duk da angizon da kasashen China da Rasha da ake samu a kasashen Afirka.
Duk da cewa ba a samu sakamako mai ma’ana bayan shekaru tara na kasancewar sojojin kasa-da-kasa a Mali ba, amma salon mulkin gwamnatin soja da Assimi Goita ke jagoranta bai kawo sauki a hulda a fannin tsaro da kasashen Yamma irin Jamus ba.
A wata hira da Gidan Rediyon Jamus, Wendyam Sawadogo, masanin siyasa da ke aiki da cibiyar bincike ta kasar Holland wato Clingendael Institute, ya yi gargadin cewa karuwar tasirin da Rasha ke da shi a yankin Sahel, zai karu idan Jamus ta janye sojojinta a Mali.
Irin wannan dalili ne ya sa hukumar horar da sojoji ta Turai EUTM ta daina aiki a Mali kuma yanzu haka ta karkata akalar aiki zuwa Jamhuriyar Nijar, saboda akwai alamu gwamnatin Mohamed Bazoum na goyon bayan kasashen yammancin duniya.