Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta sauke nauyin bashin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) saboda gudun yanke wa Fadar Shugaban Kasar wutar lantarki.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kamfanin ya sanya Fadar Shugaban Kasar a cikin jerin wuraren da kantar bashin kuɗin wutar lantarki ya yi wa katutu a babban birnin kasar.
- Direbobin dakon man fetur sun dakatar da yajin aiki
- Putin ya bai wa Kim Jong Un kyautar mota ta alfarma
Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Bayo Onanuga, mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya ce za a biya bashin kuɗin wutar lantarkin nan da ƙarshen wannan mako.
Sai dai Mista Bayo ya ce bashin kuɗin wutar lantarkin bai wuce N342, 352, 217.46 ba, sabanin ikirarin da kamfanin na AEDC ya yi na cewa bashin ya kai Naira miliyan 923.
A cikin wata wasika mai kwanan watan 14 ga Fabarairun 2024 da AEDC ya aike wa Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa kuma aka wallafa a wasu gidajen jaridu, yana bin Fadar Shugaban Kasar bashin kuɗin wutar lantarki har Naira miliyan 923.
A cewar Mista Bayo, “bayan sulhu da aka yi tsakanin bangarorin, an cimma matsaya kuma kowanne ya gamsu, inda Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ya ba da tabbacin cewa za a biya AEDC bashin kafin karshen wannan makon.
“Saboda haka ana fatan wannan zai zama abin misali ga sauran ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnati da su daidaita da Kamfanin AEDC domin biyan bashin kuɗaɗensu na wutar lantarki.”