’Yan Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu na shirin yin muhawara kan tisge shugaban kasar, Cyril Ramaphosa, kan zargin badakalar wasu kudade.
Ramaphosa wanda zargin rashawa ta dabaibaye magabacinsa, Jacob Zuma, na fuskantar barazanar tisgewa kan wasu kudade da ake zargin ya yi sama da fadi da su.
- Zan kawo karshen ’yan bindiga cikin kankanin lokaci —Tinubu
- NAJERIYA A YAU: IPOB Ko Gwamnati: Wa Ke Iko Da Kudancin Najeriya?
Rahoton binciken wani kwamiti na musamman ya nuna shugaban kasar na iya fuskantar tsattsauran hukunci idan aka same da shi da laifi, wanda za a yi muhawara a kai da misalin karfe 12:00 agogon GMT a Cape Town.
An bukaci ’yan majalisa da su amince a ci gaba da binciken Shugaba Ramaphosa ko kuma a kasin hakan.
Shugaban mai shekara 70 a duniya na iya tsallake rijiya da baya, bayan da ya samu goyon bayan jam’iyyarsa ta ACN a satin da ya gabata, inda ta kada kuri’ar goyon baya 230 daga cikin 400 na ’yan majalisar dokokin kasar.
Sai dai wasu na ganin ba lallai ya tsallake a wannan karon ba, duba da yadda zargin da ake masa ya dauki dumi a majalisar sannan wasu daga tsagin jam’iyyarsa ta ACN na goyon bayan a tsige shi.
Shugaban jam’iyyar, ya yi wasu kalamai cewa za su yi watsi da duk wani yunkuri na tilasta wa Ramaphosa yin murabus daga mukaminsa.
Sai dai kalaman sun harzuka wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar, inda suka ce dole bangaren zartarwa ya tilasta sa hannu kan sa Ramaphosa yin murabus.
Jam’iyyun adawa dai na ci gaba da yin zazzafar adawa kan dole a binciki Ramaphosa tare da gurfanar da shi a gaban shari’a.
Kuri’ar tsigewar, ita kanta na bukatar goyon bayan akalla kashi biyu bisa uku na ’yan majalisar kafin tsige shugaban.
Shugaban wanda hamshakin attajiri ne kafin ya shiga siyasa, ya samu kansa a cikin tsaka mai wuya a watan Yuni lokacin da tsohon jami’in leken asiri na Afirka ta Kudu, ya kai karar sa ga ’yan sanda.
Arthur Fraser ya yi zargin Ramaphosa ya yi sama da fadi da miliyoyin kudi a 2020.
’Yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike, amma kawo yanzu ba a tuhumi Ramaphosa da wani laifi ba, kuma shi kansa ya musanta duk zarge-zargen da ake masa.
Ya tabbatar da sace Dala 580,000 da aka boye a karkashin wata katifa a gonarsa, sai dai ya ce kudin kasuwancin wasu shanu ne da wani dan kasuwa dan kasar Sudan ya saya.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki uku kafin Jam’iyyar ANC ta gudanar da taronta na shekara biyar domin zaben sabon shugaban da zai jagorance ta.