✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana musayar yawu tsakanin Gwamna Lawan Dare da Matawalle

Abin takaici ne yadda ake siyasantar da matsalar tsaron Jihar Zamfara.

Jihar Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar ’yan fashin daji masu kashewa da satar mutane domin kuɗin fansa.

Sai dai kuma wasu na ganin rikicin siyasar Zamfara ya yi tasiri wajen ta’azzara matsalar tsaron tare da kawo cikas ga ƙoƙarin samun nasarar kawar da ita, bayan ganin yadda Gwamnan jihar Dauda Lawan Dare da kuma tsohon Gwamnan jihar kuma ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle sun fito suna suka da caccakar junansu.

Da farko, Gwamna Dauda ne ya buƙaci Matawalle ya yi murabus a muƙaminsa na minista har sai ya wanke kansa, yana mai zarginsa da taimaka wa ’yan bindiga ta hanyar gayyatar su gidan gwamnatin jihar da kuma biyan su kuɗin fansa daga lalitar gwamnati.

Sai dai a martaninsa, Matawalle ya musanta zargin tare da cewa shi kaɗai ne ya rantse da Alkur’ani cewa, ba shi da alaƙa da ’yan bindiga.

Sannan ministan ya ƙalubalanci wanda ya gaje shi ya fito ya rantse da Alkura’ni mai tsarki cewa, ba shi da hannu a matsalar tsaron Zamfara.

Shi ma ɓangaren Sanata Abdul’aziz Yari na Jam’iyyar APC ya fitar da sanarwa ta martani ga Gwamna Dauda na Jam’iyyar PDP game da kalamansa kan Matawalle.

Cikin sanarwar, Abdul’aziz Yari ya gargaɗi Gwamna Dauda cewa, ya daina ɗora laifin matsalar tsaro kan Bello Matawalle, ya mayar da hankali ga aikinsa.

Sai dai a nata martanin, Jam’iyyar PDP a Zamfara ta ce, Bello Matawalle ya kamata Sanata Yari ya ba wa wannan shawarar.

Ɓangarorin biyu sun daɗe suna sukar juna kan lamuran da suka shafi Jihar Zamfara tun bayan zaɓen 2023 da Dauda Lawan Dare na Jam’iyyar PDP ya kayar da Bello na Jam’iyyar APC.

Masana na ganin wata al’ada ce ga duk gwamnan da ya hau idan ya gaji matsala zai rika dora matsalar ne ga wanda ya gada.

Domin shi kansa Bello Matawalle lokacin da yana gwamna ya zargi wanda ya gada Abdul’aziz Yari.

“Yanzu kuma ga shi yana sa-in-sa da wanda ya gaje shi, Gwamna Dauda don haka ba sabon abu ba ne a siyasar kasar nan,” in ji Barista Audu Bulama Bukarti mai sharhi kan lamuran yau da kullum kuma masanin sha’anin tsaro a Nijeriya.

“Duk ƙarfin mutum idan har aka fito da ƙwararan hujjoji kan manyan zarge-zargen taimaka wa ‘yan ta’adda da za su gamsar da masu hankali, dole gwamnati ta ƙaddamar da bincike.

“Idan ya kasance ana jifan juna da irin waɗannan maganganu kuma babu wata hujja a kansu, babbar matsala ce ga ƙoƙarin samun nasara kan matsalar,” in ji masanin.

Ya ce, babban abin takaici ne irin sa-in-sar shugabannin siyasa a Zamfara domin harkar tsaro ba harkar siyasa ba ce.

Ya ƙara da cewa, da gwamnan jihar mai ci da kuma ƙaramin Ministan Tsaro babu wanda Allah ya ɗora wa alhakin matsalar tsaron Zamfara kamar su biyu.

Alhakin tafiyar da gwamnatin jiha na kan gwamna, yayin da kuma ƙaramin Ministan Tsaro, wakili ne na Jihar Zamfra a tarayya. Amma kuma sai ga shi an ga sun koma suna caccakar juna.

Rashin tsaro matsala ce da ta shafi kowa, ta shafi PDP ta shafi APC da dukkanin ƙabilu da addinai.

‘‘Don haka abin takaici ne yadda ake siyasantar da matsalar tsaron maimakon su hada kansu su yaki matsalar,” in ji Barista Bukarti.