An harba bindigogi da barkonon tsohuwa a ginin Majalisar Dokokin Jihar Ribas da ke Fatakwal, bayan wasu ’yan majalisar sun fara kokarin tsige Gwamnan Jihar, Siminalayi Fubara.
Bayan barkewar harbe-harben dai, mutane sun rika guduwa domin tsira da rayukansu, yayin da jami’an tsaro suka rika kora mutane, ciki har da ma’aikatan da ofisoshinsu ke cikin harabar majalisar.
- Cin Gashin-Kai: An rufe Majalisar Dokokin Gombe
- Ya kamata Najeriya ta fara tsarin mulki na shekara 6, babu tazarce
Bayanai sun nuna yanzu haka, ’yan majalisa 23, cikin har da shugaban majalisar, Martin Amaewhule, sun fara shirin tsige Gwamnan.
Kazalika, majalisar ta kuma tsige Shugaban Masu Rinjayenta, Edison Ehie, wanda ake zargin yana tare da Gwamnan.
Idan za a iya tunawa, ko a daren Lahadi sai da wasu da ake zargin hayar su aka dauka suka banka wa ginin majalisar wuta.
Jim kadan da aike wa Gwamnan takardar tsigewar dai, an ga ’yan majalisar wajen misalin karfe 8:15 suna ficewa cikin tsauraran matakan tsaro.
Lamarin dai ya dada tabbatar da zargin da ake yi na lalacewar alaka da Gwamna Fubara da tsohon maigidansa kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike.