Wata yarinya mai kimanin shekara 6 da take wakiltar Jihar Bayelsa na daga cikin wadanda ake fafatawa da su a gasar wasanni ta kasa karo na 19 da ke gudana a Abuja
Yarinyar mai suna Deborah Kuickpen tana fafatawa ce a wasan dara na Chess tare da mahaifiyarsa mai shekara 56.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Premium Times ta kalato, Deborah ce mafi karancin shekaru a gasa yayin da mahaifiyarta Taofeek Maya kuma mai shekara 56 ita ce mafi yawan shekaru a gasar. Dukansu suna wakiltar Jihar Bayelsa ne a wasan Chess.
Deborah ta ba mutane sha’awa da mamaki, ganin yadda take da karancin shekaru amma ake fafatawa da ita a gasar.
An ga yadda take ba manya kashi a wasan Chess ba tare da fargaba ko shakka ba, kuma burinta lashe lambar yabo kafin a rufe gasar a jibi Lahadi.
A zantawar da aka yi da mahaifiyar Deborah, Misis Taofeek Maya, ta ce Deborah tun tana ’yar shekara 2 take sha’awar yin wasan Chess kuma ta kware ne a lokacin da ta kai shekara 6 da hakan ya sa ta nemi Jihar Bayelsa ta sanya ta cikin ’yan wasan da za su fafata a gasar wasanni ta kasa karo na 19 da ke gudana a Abuja.
A nata bangaren Deborah ta ce burinta shi ne ta lashe lambar zinare a wannan gasa. Kuma tana fata ta wakilci kasar nan a gasar Olamfik ta duniya a wasan Chess a nan gaba.