✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a Ekiti

INEC ta bayyana cewa za ta fara aiki da sabon tsarin wallafa sakamakon zabe kai tsaye ta na’ura mai kwakwalwa.

A ranar Asabar ce aka kada kuri’ar zaben gwamnan Jihar Ekiti, inda jama’a suka rika fitar dango zuwa jefa kuri’arsu ta zaben sabon gwamnan da zai jagoranci jihar tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Aminiya ta ruwaito cewa, an tsaurara matakan tsaro tun gabanin zaben, inda ya zuwa yanzu an rufe rumfunan zabe da dama bayan kammala jefa kuri’u kuma har an soma tattara sakamako.

Duk wanda ya yi nasara a zaben zai maye gurbin gwamna mai barin gado Kayode Fayemi na jam’iyyar APC, wanda a cikin shekarar nan wa’adin mulkinsa zai kare.

An gudanar da zaben a rumfunan zabe akalla dubu 2 da 445 wanda hakan ya bai wa jama’a damar jefa kuri’un zaben sabon gwamnan a jihar ta Ekiti mai Kananan Hukumomi 16.

Yadda ake zaman tattara sakamakon zabe daga ofishin INEC na Karamar Hukumar Oye

Kawo yanzu dai fafatawa tafi zafi tsakanin da takarar jam’iyyar APC mai mulki, Abiodun Oyebanji da kuma tsohon gwamnan jihar, Segun Oni, dan takarar jam’iyyar SDP, sai kuma dan takarar PDP, Bisi Kolawole.

Tun a watan Janairu ne jam’iyyu suka gudanar da zabukan fitar da gwanayensu, kuma sunayen wadanda Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta tantance ne kawai suka kasance a kan takardun kuri’ar zaben.

A halin da ake ciki, tuni INEC ta bayyana cewa za ta fara aiki da sabon tsarin wallafa sakamakon zabe kai tsaye ta na’ura mai kwakwalwa a zaben gwamnan na Ekiti da ya gudana, karon farko da aka aiwatar da sabon tsarin zaben, tun bayan sabuwar Dokar Zabe da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu.

Gabanin zaben na yau, alkaluman hukumar ta INEC sun nuna cewar mutane fiye da dubu 700 ne suka cancanci kada kuri’a a zaben.

Matakan da ake bi wajen tattara sakamakon zaben Ekiti

Mataki na gaba da aka shiga a zaben gwamnan Jihar Ekiti bayan kammala kada kuri’a da kuma kirga su a wasu rumfunan zabe shi ne tattara sakamakon.

Tattara sakamakon na nufin hada kan lissafin adadin kuri’un da aka samu a rumfunan zaben tare da hada su wuri guda.

Kowane bangare na da turawan zabe da INEC ta nada da za su gudanar da shi. Su ne kamar haka:

Baturen zabe na rumfar zabe zai tura sakamakon zaben zuwa wurin tattara sakamako na mazaba sannan shi kuma jami’in tattara sakamako zai karba ya aika matattarar sakamako ta Karamar Hukuma.

Daga nan jami’in tattara sakamako na Karamar Hukuma zai aika wa baturen zabe na jiha, inda shi kuma baturen zabe na jiha zai tattara sakamakon daga Kananan Hukumomi kuma ya sanar da su, sannan ya bayyana wanda ya yi nasara a zaben gwamnan.

Yadda za a sanar da zakara a zaben

INEC ce dai ke da alhakin sanar da wanda ya yi nasara a zaben gwamnan Jihar Ekiti, wanda a cewarta za a sanar da wanda ya yi nasara ne kawai idan dan takara ya samu mafi rinjayen kuri’un da aka kada a zaben.

Haka kuma INEC ta gindaya sharadin cewa kar dan takara ya gaza samun kashi daya bisa hudu na dukkan kuri’un da aka kada a akalla kashi biyu bisa uku na dukkan Kananan Hukumomin jihar.