Da yake mayar da jawabi kan zargin da kungiyoyin ma’aikatan jami’ar suke masa, shugaban jami’ar Farfesa Alhassan Muhammed Gani, cewa ya yi shi bai karbi kowanne irin koke daga wajensu ba, domin yanzu yake samun labarin daga ‘yan jarida. Abin da ya sani kawai shi ne jami’a tana biyan albashi yadda ya kamata.
Farfesa Gani, ya ce suna samun karancin kudi na biyan albashi domin sai an nemi ciko sannan a biya albashi, wannan ma a watan Fabarairu ne kawai amma wannan din ma yanzu an wuce wajen.
Ya kuma kara da cewa kamar yadda suke kukan rashin biyan albashin watan Oktoba, wannan kan ba a biya ba kuma ba jami’ar Kashere ce kadai ba ta biya ba sauran jami’oi ma ba su biya ba saboda an dan samu canji ne daga Gwamnatin Tarayya kuma duk lokacin da aka sake kudin za a biya.
Sannan albashin watan Mayu da aka biya sau biyu ake neman su dawo da shi, an biya ne a watan Agusta, inda ya ce ya yi magana da shugabannin kungiyoyin ta wajen magatakardar jami’ar kan cewa kar su taba, an biya ne da kuskure za su dawo dasu amma suka kashe.
Daga nan sai Farfesa Alhassan Muhammed Gani, ya ce shi bai kulle jami’a ba kamar yadda suke cewa za su je yajin aiki na mako uku,ya ce shi ba ruwansa, duk wanda yake ganin zai je yaje ya bar masu karatu su yi karatunsu shi bai kulle makaranta ba.
Kungiyoyin dai sun kira membobinsu kan cewa su tafi yajin aiki na makonni uku tare da kulle ko’ina a jami’ar har ofishin shugaban jami’ar.