Ofishin Kula da Basuka na Kasa (DMO) ya ce yawan basukan da ake bin Najeriya ya karu zuwa tiriliyan 31 a watan Yuni, 2020.
Ofishin ya ce basukan za su karu a bana saboda rancen da kasar ke nema daga kasashen duniya.
- Bashin da aka karbo daga Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da sauransu ne suka sa yawan bashin karuwa zuwa Naira tiriliyan 31.
- Hukumar kula da dukiyar masu taurine bashi (AMCON) ta kwace bashin sama da miliyan N600na Hydro Hotels over N600m debt
Ana ganin yawan bashin zai karu a bana saboda rancen da za a karbo daga hukumomin kasashen duniya.
- Matattun ma’aikata 333 ne ake karbar albashi da sunansu a Jihar Neja
- Najeriya ta kusa durkushewa a hannun Buhari
Zuwa watan Maris 2020, bashin ya kai tiriliyan N28.6 wanda ya kunshi dukkannin basukan Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Birnin Tarayya.
A baya-bayan nan yawan bashin ya kai tiriliyan N31.009 ya kai Dala biliyan 85.897, yayin da tiriliyan N28.628 na watan Maris ya kai biliyan N79.303.
Dalilin karuwar
Bashin ya karu da tiriliyan N2.38 (Dala biliyan 6.59) a cikin wata uku.
Basukan sun karu ne sakamakon karbo rancen Dala biliyan 3.36 daga Asusun Lamuni na Duniya (IMF) domin aiwatar da kasafin kudi; karin basukan da aka karba a cikin gida domin samar da kudaden aiwatar da sabon kasafin 2020; takardun rance na Sukuk; da kuma takardun Promisory notes da aka bayar domin biyan hakkokin masu fitar da kaya zuwa kasashen waje.
Abubuwan da basukan suka kunsa:
Basukan da aka karbo na tiriliyan N16.360 daga kasashen waje su ne kaso mafi tsoka (kashi 51.97%) na bashin da Najerya ta karbo.
An karbo basukan ne daga IMF, Bankin Duniya, Bankin Raya Afirka (AfDB), Eurobonds da basukan kasashen waje na Diaspora bonds.
Rance daga kasahen waje ya kai tiriliyan N3.948, kashi 12.54% na bashin da aka karbo daga hukumomin raya kasashe na Sin, Faransa, Japan, Indiya da Jamus.
Kashi na uku shi ne rancen kasuwancei na tiriliyan 11.168, kashi 35.48%. Wannan shi ne na biyu wurin yawa bayan wanda aka karbo daga hukumomin duniya da Eurobonds da kuma rancen Diaspora bonds.
Ci gaba da karuwar bashin:
Rancen da ake shirin karbowa daga Bankin Duniya da AfDB da Bankin Raya Kasashe na Musulunci (IsDB) domin aiwatar da kasafin 2020 zai sa bashin da ake bin kasar karuwa.
An ba wa hukumar kwastam ta kasa wani bangare na kudin domin zamanatar da ayyukanta a tashoshin jiragen ruwa da Dala tiriliyan 3.1.
Yawancin basukan masu dogon zango ne da aka riga aka fara biya, sauran kuma sabbi ne da za a fara biya daga 2022.
Wa’adin kammala biyan bashin Sukuk da sauran rancen cikin gida shekara biyar zuwa bakwai ne.
Bashin da ake binka
Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ta ce an yi tsare-tsare domin biyan basukan. Kasafin kudin 2020 ya ware fiye da tiriliyan N3, kusan rubu’in kasafin domin biyan basuka.
Idan aka raba bashin tiriliyan 31 a tsakanin ’yan Najeriya da yawansu ya kai miliyan N200, to ana bin kowane dan kasar bashin N155,000.
Bashin zai kara yawa idan aka karbo rancen Bankin Duniya da AfDB da IsDB na gaba a wannan shekarar.