Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya yi zargin ana barazana ga rayuwarsa da ta wasu daga cikin mukarrabansa.
Ya ce ana yunkurin ne saboda Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar ya yi aiki da sharwarar da kwamitin da aka kafa don ya binciki zaben fitar da gwanin mazabar Ahiazu Mbaise a Majalisar Jihar Imo.
- Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasar APC
- Za mu kashe N2bn kan tantance ma’aikatan makarantu —UBEC
A cikin wata sanarwa da ya fitar ta bakin kakakinsa, Ikenna Onuoha, Sanata Samuel ya ce wasu da soke zaben bai yi musu dadi ba suka fara barazanar za su kashe shi.
A cewarsa, tun lokacin da ya zama Sakataren PDP, wasu suka fara aika masa da barazana iri-iri don su kai shi kasa.
Ya ce mutanen sun kuma yi barzanar rufe ofishin Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) da ke Jihar, sannan su lalata duk wani ginin gwamnati ko duk abin da ke da alaka da shi.
Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan sandan Jihar ta Imo, CSP Mike Abatam, ya ce har yanzu ba su karbi korafin dan siyasar ba ab hukumance.