A ranar Larabar da ta gabata ce Allah Ya yi wa sanannen mawakin nan na Jamhuriyar Nijar, Mamane Barka rasuwa a Yamai babban birnin kasar.
Tuni dai dumbin mutane a Nijar da Najeriya suka fara bayyana jimaminsu na mutuwar tasa. Marigayin mai shekaru 60 da haihuwa, ya bar mata daya da ’ya’ya 10.
An haife shi a shekarar 1959, ya kuma yi fice wajen yin wakokin gargajiya ta hanyar amfani da gurmi cikin harsunan Hausa da Faransanci, inda har aka san shi a duniya.
Amma a shekarar 2002, sai ya sauya hanya saboda samun daukar nauyin karatu daga Hukumar UNESCO, inda samu halartar Makarantar Nazari Kan Harkokin Afirka a Landan na Kasar Ingila.
Marigayin ya yi amfani da kudinsa wajen sake farfado da kida ta amfani da biram, wanda mutanen Boudouma suke amfani da shi.
Barka ya sa irin wannan kida ya yi tashe, inda ya ja hankalin duniya a kan yadda yake amfani da kayan kidan da ya harhada shi da kansa a shekarar 2009.