Wata ’yar ƙasar Faransa mai shekara 68 za ta shafe shekara guda a kurkuku, saboda ajiye kyanwoyi 159 da karnuka 7 a cikin ɗakinta.
Matar da ba a bayyana sunanta ba tare da mijinta mai shekara 52 sun samu saɓani da maƙwabta a gidansu saboda ƙazantar da dabbobin suka haddasa.
- Hatsarin Jirgi: Dana Air ya sallami ma’aikata
- ‘Yaron da ya sayar da ƙodarsa ya sayi wayar hannu ta N290,000’
Daga ƙarshe an kira ’yan sanda waɗanda yanayin gidan matar ya girgiza su.
Akwai najasar dabbobin a ko’ina, fiye da kyanwoyi 150 da karnuka bakwai da kuma aƙalla matattun kyanwa biyu da karnuka biyu aka iske a cikin ban-ɗakinsu.
Da yawa daga cikin dabbobin sun rame, suna fama da rashin abinci mai gina jiki, ko sun kamu da cututtuka, wasu kuma daga baya sun mutu saboda rashin lafiya.
Matar ta yarda cewa ta “ɗaure dabbobin” yayin da take ƙoƙarin kula da dabbobinta da dama, amma ta bayyana dabbobin a matsayin “soyayyar da take wa rayuwarta.”
Matar ta shaida wa masu bincike cewa matsalarta ta faro ne tun a shekarar 2018, bayan da ta ɗauki kyanwoyi uku da karnuka uku na iyayenta. Ba da daɗewa ba ta fara ceto kyanwoyin da suka ɓace su 30.
Bayan wani lokaci, dabbobin suka fara haifuwa, kuma a lokacin da ’yan sanda suka shiga gidanta a bara, tana da kyanwoyin da ba su gaza 159 ba.
Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ta ajiye dabbobin duk da ta san ba za ta iya kula da su yadda ya kamata ba, sai ta ce, saboda ana yin watsi da dabbobin ne.
Bayan tantance lafiyar ƙwaƙwalwarta, an gano matar tana da sha’awar tara dabbobi ne kawai, inda aka bayyana hakan a matsayin wata buƙata ta hankali ta kula da ceto dabbobi, wanda ba kowa zai iya yin haka ba.
Don hana ta sake faɗawa cikin yanayin laifin rashin kula da dabbobin, alƙali ya ba da dokar hana ta kiwo dindindin. An kuma umurci matar da mijinta su biya Dala 160,000 (kimanin Naira miliyan 205 dubu 120) ga ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi da wasu ƙungiyoyin farar hula.