✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yaron da ya sayar da ƙodarsa ya sayi wayar hannu ta N290,000’

Yaron ya tura wa mai sayar da wayar hannun kudi fiye da kima.

Daya daga cikin yaran da aka cirewa ƙoda a wani asibiti a Abuja ya je sayen wayar salula ta kimanin naira 290,000 kwanaki bayan sayar da ƙodarsa.

Wani mai sayar da waya a kasuwar Mararraba da ke Jihar Nasarawa, Abdullahi Mohammed ne ya shaida wa Babbar Kotun Abuja yayin da ya bayyana a matsayin daya daga cikin shaidun da aka gabatar mata a ci gaba da shari’ar takaddamar cin kasuwar ƙoda a babban birnin kasar.

Abdullahi Mohammed ya shaida wa kotun cewa, Oluwatobi Salmon Adedoyin ya zo shagonsa ne a ranar 20 ga Fabrairu, 2023 don siyan wayar har ta kusan Naira 290,000.

Da yake gabatar da shaidar a ranar Alhamis, lauyan masu ƙara, Hassan Tahir Esq ya ce Abdullahi Mohammed wanda aka je sayen wayar salular a shagonsa ya bai wa yaron bayanan asusun ajiyarsa na banki inda aka tura masa kuɗi Naira 500,000.

“Na tambaye shi dalilin da ya sa ya biya ni fiye da kima, sai ya ba ni asusun ajiyarsa na bankin Opay don in mayar da kuɗin da ya kai Naira 210,000 ya tafi abinsa,” in ji Abdullahi.

Tun da farko, lauyan ƙara, Tahir ya sanar da kotun cewa ba zai iya kammala gabatar da hujjojinsa ba saboda rashin halartar jami’in da ke bincike a kan lamarin.

Hakazalika, lauyan wanda ake ƙara, Afam Osigwe (SAN) ya buƙaci kotun da ta sauya ranar ci gaba da sauraron ƙarar zuwa lokaci na gaba domin samun damar tattaro hujjojinsa.

Dangane da wannan bukatar ce mai shari’a Kezziah Ogbonnaya ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 da 22 ga watan Mayu.

Ana iya tuna cewa, Hukumar Hana Fataucin Mutane Ta Ƙasa (NAPTIP) ce ta gurfanar da wasu ma’aikata huɗu na asibitin Alliance and Service Ltd a gaban ƙuliya, ciki har da Dakta Christopher Otabor da Emmanuel Muyiwa Olorunlaye da Chikaodili Ugochukwu da kuma Dakta Aremu Abayomi a kan tuhume-tuhume 11 da ke da alaƙa da safarar sassan jiki ba bisa ƙa’ida ba.

Wannan na zuwa ne dai bayan wani rahoton fallasa da Jaridar Daily Trust ta wallafa bayan ta bankado yadda ake cinikin sassan jikin mutum a Abuja da Jihar Nasarawa bayan bincike da tattaunawa da waɗanda abin ya shafa.